An kafa Asusun Tara Rarar Ribar Danyen Mai ne domin a rika tara kudade daga cikin ribar danyen mai ana adanawa. Hikimar kafa wannan asusu ita ce, a duk lokacin da aka samu gibi, cikas ko karancin kudaden da za a gudanar da ayyukan da ke cikin kasafin kudi, to sai a kwasa daga cikin wannan asusu, asiri rufe ayi amfani da su.
Najeriya ta tara Dala Biliyan 109.37 da yayi daidai na Naira Tiriliya 15.274 a Asusun Tara Ribar Rarar Mai daga 2004 zuwa 2018.
A dalilin tashin gwauron zabi da farashin danyen mai yayi an samu tulin karin kudade a dake shigar asusun ribar mai kusan ninki uku daga 2005 zuwa 2008. Sannan asusun ya haura daga Dala Biliyan N5.9 a 2005 zuwa sama Dala Biliyan N17 a 2008.

A zamanin gwamnatin Obasanjo, an tara akalla Dala Biliyan $33.74 a wannan Asusu daga 2004 da 2006. Shi ko Yar’adua an tara Dala biliyan $27.36 sannan ya kashe Dala biliyan $28.73.

Kwatankwacin kudaden da aka tara a Asusun ECA daga shekarar 2004 zuwa 2018 ya kama Naira Tiriliyan N4.36, inda kasafin kudin kasa a wannan shekaru ya kai Naira Tiriliyan N4.8.
A tsakanin 2010 zuwa 2014, Asusun ECA ya tara Dala Biliyan $45.56 da yayi daidai da Kasafin kudin kasa a wannan lokaci wato Naira Tiriliyan N23.47.
Jimillar Kasafin kudin kasa daga 2015 zuwa 2018 ya kama Naira Tiriliyan N27.11. Naira Tiriliyan N4.49 a 2015, Naira Tiriliyan N6.08 a 2016, Naira Tiriliyan N7.44 a 2017 sannan Naira Tiriliyan N9.1 a 2018.
