Bayan godiya da yabo ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban halitta, Annabi Muhammad Sallahu Alaihi wa Sallam. Bayan haka
yaku bayin Allah, ina muku wasiya da ni kaina da jin tsoron Allah.
Kuji tsoron Allah, kuyi aiki da magana na gaskiya. Allah zai daidata lamarinku kuma ya gafartamuku zunubbanku, duk wanda yabi Allah da
manzonsa, hakika zai samu babban rabo a duniya da lahira.
Yaku bayin Allah! Ita barna, wato ibinda muke kira da CORRUPTION ita ce duk abinda yake ba daidaiba a cikin magana, ko aiki, ko sana’a , ko
shugabanci, ko mulki, ko siyasa, ko ibada, ko zamantakewa, ko kasuwaci, dukkannin abinda ya sosa zuciya kuma mutum baya jingina kansa
da shi, duk abinda ya ke sabanin abu mai kyau, shi a ke kira da FASADI a musulunce.
CORRUPTION yaku bayin Allah! Shi ne Barna a bayan kasa, yana da illa fiye da wutar daji mai hallaka komai kuma babu abinda ke tsayar da
ita. Allah yayi nuni da shi a cikin Al-Kur’ani “Mutane sun bayyanar da barna (CORRUPTION) a cikin ruwa da tudu, domin barnarsu, Allah zai danda namusu sakamakon aikinsu, ko za su dawozuwa ga tafarki madai-daici”. Ya ku ‘yan uwa a cikin imani! Munbar CORRUPTION (barna)
ya yi katutu acikin al’umma. Maza damata, yara da manya, talakawa da mawadata, shugabanni da mabiya, malamai da jahilai, ‘yan birni da na
kauye. Kowa na tafka barna (CORRUPTION) a cikin rayuwar sa na neman duniya ko na neman lahira.
Lalacewar al’uma da tahanyan CORRUPTION shi ne ya haifar da durkushewar arzikin kasarmu Nigeria, duk da tullin arzikin da Allah ya
yiwa wannan kasa, kididdgar duniya ya tabbatar da mune hedikwatar talauci ta duniya, mune mukeda mafi yawan yaran da basu zuwa
makaranta, sabo da lalacewar ilimi, kiwan lafiya ya tabarbare, ga rashin aikin yi, ilimi ya lalace, babu tsaro, garkuwa da mutane, sara
kuka, cutuka, mace-mace, karuwanci da sauran masifu iri daban-daban, sun dabaibaye wannan kasa sakamakon fasadin da Allah ya yi hani da
shi.
Hadisi ya tabbata cewa: abuwa biyar Annabi SAW yana neman tsari kar a jarabemu da su, kaicon mu!!! dukkansu munyi nesa a cikinsu, har
janzawa haramun suna muke yi a Najeriya. Guda uku su ne suka shafi (CORRUPTION) kuma su suka jefa mu acikin halin ni’yasu:
1 – Duk al’umar da ta bayyana barna wato CORRUPTION Allah zai saukarmata da bala’in cutuka, a yau dai cutuka sun damu mutane, an rasa magani, ko maganin yaki aiki, ko ciwon yaki warkewa ga tsadar magani da neman lafiyar duk sakamakon fasadi ne a bayan kasa. Dai–dai ne ‘yan Najeriya su keda cikkakiyar lafiya, kowa da abinda ke damunsa.
2 – Duk al’umar da ta tauye ma’auni (wato tauye mudu ga ‘yan kasuwa, ko rashin cika ka’idojin aiki ga ma’aikata da masu sana’a) Allah zai jarabeta da yunwa, hadima dawainiya, murdiya da zaluncin shugabanni. Yunwa ta bayyana har kan mawadata sabo da ciwon ulcer, bini –bini kadan cin abinci.
3 – Duk al’umar da suka ki bin dokokin Allah, Allah zai jarabesu da junansu. Duniya tayi ittifakin Najeriya kasace ta addini (Musulunci
/Kiristanci), kasace da tafi kowace kasa son addini, yawan masallatai, yan coci. Amma mun watsar da dokokin addini, sai muka zamo masu kashe juna da sunan addini, muke sata a masallaci, coci, da makabartu, muke tare hanya mukashe, mukashe mutane a gurin ibada. Bala’i tsakanin abokai, tsaknin ‘ya’ya da iyaye, tskanin mata da miji, tsakanin ‘yan-uwa, tsakanin makwabta, tsakanin kabilu, duk wannnan fa domin
munyi watsi da dokokin Allah ne ta hanyar (corruption) barna a bayan kasa.
Dama Allah ya ja mana kunni, inda ya ke cewa, Duk wanda ya kauce daga dokokin Allah, to lalle zai yi kuntatacciyar rayuwa a duniya, kuma a tashe shi makaho ranar kiyama.
Ya ku ‘yan Najeriya, kun kutsawa (CORRUPTION) Cin Hanci Da Rashawa, kasarku ta lalace a idon duniya, kuma kun zamo kaskantattu
a kasashen duniya, ana muku kallon azzalumai, mabarata, wulakantattu, marasa gaskiya. Kun talauta kasarku da al’umarku duk da arzikin da
Allah yayi muku. Mutane nawa ne suka fi jahohinsu arziki a ko wace jaha? Duk mai hankali yasan kasarnan na cikin mummuna hali. Idan ba mu
gyaraba Allah zai kawar da mu, ya maye gurbinmu da wasu.
Bayin Allah! Lalle Allah ba ya canzawa wata al’umma har sai ta canza ma kanta. Lalle mu canza, Allah zai canza mana da alhairinsa, mu tuba
daga zunubbanmu, Allah zai gafarta mana. Mu gyara kawunanmu, mu yaki CORRUPTION, mu yi kyawawan ayyuka, domin suna shafe munana. Mu
kyautata, Allah yana son masu kyautatawa. Idan muka gyara Allah zai yafe mana, ya dawo mana da martabarmu, da arzikinmu, da kwanciyar
hankalinmu da zaman lafiyanmu. Allah ka taimakemu da shugabbaninmu, kai mana albarka da al’umarmu, ka gafarta mana da iyayenmu, Lalle kai
mai iko ne akan komai.
TAKAITACCIYAR FASARAR HUDUBAR MASALLACIN HARAKATU FALAHIL ISLAM, BARNAWA LOW COST KADUNA. DAGA IMAM MUHAMMAD BELLO MAI-IYALI
MAI TAKEN CORRUPTION YAFI GOBARAR DAJI BARNA
Tarar Juma’a, March 29, 2019 (Rajab 22, 1440)