BIDIYO: TA’ADDANCI A AREWA: Mu fito mu gaya wa gwamnati da manyan Arewa gaskiya, “Ana sace mutane kamar kaji” – Zaharaddeen Sani

0

Fitaccen Jarumin Kannywood Zaharaddeen Sani cikin fushi ya yi kira ga abokanan aikin sa musamman mawaka da su fito su nuna bacin ran su bisa yadda ayyukan ta’addanci ke neman ya lashe yankin Arewacin Najeriya.

Zaharadden a wani Bidiyo da ya aika wa PREMIUM TIMES, ya bayyana cewa ayyukan ta’addanci da sace-sacen Mutane ya addabi yankin da a halin da ake ciki abin ya kai ga sai dai Lahaula.

” Ku duba yadda ake sace mutane a titin Abuja zuwa Kaduna, abu kamar kaji. Sai a tattara mutane masu yawa a kada su cikin kungurmin daji babu abin da ake yi akai. Wannan tashin hankali har ina.

” Ya kamata mu fito mu gaya wa gwamnati gaskiya. Yanzu da zaran ka fadi gaskiya sai ace kai dan PDP ne. Amma ku duba ku gani kwanaki nawa ne da rantasr da wannan gwamnati, amma harkar tsaro ya tabarbare a yankin Arewa. Wannan matsala akwai tashin hanklai a ciki. Ku duba Zamfara, sannan yanzu Kaduna zuwa Abuja shima ya zama abin da ya zama. Tsakani da Allah haka za mu ci gaba da zama babu wanda zai fito ya gaya wa manyan Arewa gaskiya.

Idan ba a manta ba shi kan sa gwamnan jihar Kaduna ya afka wa shingen masu garkuwan. Inda tare dashi ka sa a shiga dajin don fatattakar su.

Kalli Bidiyo:

Share.

game da Author