Ban yarda da zabin Ahmed Lawan ba, nima zan tsaya takarar shugaban majalisa – Sanata Ndume

0

Bisa dukkan alamu dai jam’iyyar APC ba ta dauki darasi ba, daga rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar bayan nasarar da ta samu a zaben 2015, wanda ya yi sanadiyyar Bukola Saraki ya zama Shugaban Majalisar Dattawa tare da goyon bayan Sanatoci na bangaren jam’iyyar PDP.

Wannan goyon baya ne ya sa Saraki ya tsaya takara tare da Sanata Ike Ekweremadu na jam’iyyar PDP a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, kuma ya yi nasara.

To kwatankwacin haka ma na niyyar furuwa a yanzu haka, idan ba wani matakin gaggawa APC ta dauka ba.

Jim kadan bayan shugabannin APC sun fito daga wata ganawar sirri da Shugaba Muhammadu Buhari da kuma zababbun sanatoci, sun bayyana cewa sun amince da Sanata Ahmed Lawan ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.

Jin haka ke da wuya sai Sanata Ali Ndume ya tuma tsalle ya ce bai yarda ba, domin shi ma a matsayin sa na sanatan Arewa maso Gabas, ya fito takara, kuma sai da ya sanar wa Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole cewa ya fito takara.

Don haka Ndume bai yarda haka kawai ya tsame wani sanata shi kadai ba tare da yin zabe ba, a ce shi ne zai zama shugaba.

Ndume ya ce zabar da aka yi wa Sanata Ahmed Lawan da Hon. Gbajabiamila a matsayin Shugabannin Majalisar Dattawa da na Majalisar Tarayya, zai iya harfar da rikici a cikin jam’iyyar APC.

Da ya ke magana da manema labarai a Abuja jiya Talata, Ndume ya bayyana amincewa tsayar da Lawan a matsayin dan takara tilo, karya dokar kasa ce, kuma an karya ruhin jam’iyyar APC da dimokradiyya.

RIKIRKICE SARKA!

Sanata Ndume ya ce matsayar da APC ta dauka cewa Ahmed Lawan ne zai zama Shugaban Majalisar Dattawa, ba abin amincewa ba ne, kuma ba ma zai yiwu ba, domin ba a bi ka’idar da ta tace ba.

Ndume ya ce kafin ya yi tunanin fitowa takara, sai da ya tuntubi jama’a masu tarin yawa kuma a dukkan bangarorin kasar nan.

Daga nan sai Ndume ya ce kawai abin da ya kamata jam’iyyar APC ta yi shi ne, ta mika Shugabanin Majalisar Dattawa a shiyyar da zai fito, daga nan sai ta kyale ’yan shiyyar su fitar da wanda suka zaba da kan su.

NA FI KARFIN A LUNKE NI BAIBAI – Ndume

“Wato abin da ya sa na ce muku abin ya yi matukar ba ni mamaki, shi ne na tabbata abokan aiki na makusanta na wadanda suka goyi baya na, sun tafi a kan cewa tunda akwai tsarin da doka ta shimfida dangane da yadda za a fitar da Shugaban Majalisar Dattawa, to a kan sa za a tafi, kuma a bi har a fitar da shugaba.

DALLA-DALLA

“Ni dai gani na yi Sashe na 51 (a) na Dokar Najeriya, ya bayyana cewa: “’Yan Majalisa ne za su zabi Shugaban Majalisar Dokoki da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokoki.

“Sashe na 1 na Dokar Najeriya ya kara bayyanawa kuru-kuru cewa: “Wannan dokar kasa ta hannu kan kowane dan Najeriya da kuma kowace hukuma ta gwamnatin Najeriya.

“A can gaba ma an kara da cewa: ‘Duk wata doka da aka bijiro da ita daga bisani ba wannan ba, to ta karya tsarin mulkin Najeriya, don haka haramtacciya ce.”

NDUME KO APC

Sanata Ndume ya ragargaji shugabannin jam’iyyar APC, kuma ya nuna irin yadda kima da mutuncin shugabannin jam’iyyar ya zube a idon sa, tun daga lokacin da aka je wurin taron ganawa da Shugaba Muhammdu Buhari.

“Ni dai na sani cewa a matsayin jam’iyyar APC, wadda ke ikirarin dimokradiyya, kuma a matsayin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, wadda ke ikirarin bin komai a kan ka’ida, to hanyar da aka bi wajen fitar da Sanata Lawan a matsayin wanda suka amince zai shugaban ci majalisar dattawa, baudaddiyar hanya ce, kuma abin da ban-al’ajabi da takaici.

“Saboda hanyoyi uku ne ya kamata a bi kamar yadda doka ta tanadar: Ko dai a yi yarjejeniyar amince wa dan takara daya, a tsakanin su ‘yan takarar ya-su-ya-su, wato ‘consensus’, ko a yi zabe ko kuma gaba daya a yi zaben fidda-gwani.” Inji Ndume.

YADDA GANAWAR MU BUHARI TA KASANCE A DABAIBAYE -Ndume

“Abin takaici kuma shi ne yadda aka dauki wannan matsaya a gaban Buhari, sannan kuma aka hana mu yin tambaya ko yin wani bayani, ko neman karin haske.

“Wato ko da Shugaban Kasa ya yi na sa takaitaccen jawabin, sai kawai kafin mu farga mun ka ji aka an rangada buga badujalar taken Najeriya.

“Hatta su kan su wadanda aka ce su za a zaba din (Sanata Ahmed Lawan da Hon. Gbajabiamila), ba a ma bar su sun yi wani jawabin godiya ko ko ba mu hakuri ba.

“Ba a tuntubi ko da mutum daya daga cikin mu da muka nuna shawarar neman shugabancin ba, kuma muka aika musu da sanarwar fitowar mu takara. Ba a kuma ba mu damar yin magana a gaban Buhari ba.

AL’AJABIN APC YA SA NI DAWURWURA

“Haka na fice a cikin mamaki da al’ajabi. Amma duk da haka na samu yi barci na sosai. Na san dai ni mutum ne daya tilo a cikin sanatoci 109. Ban ce na fi sauran 108 din ba. Sai fa ko shi Sanata Lawan.

“Mata ta da ’ya’ya na sun nuna damuwar su, ni kuma ranar barci na yi, har ma na makara a lokacin sallar Asubahi.

“Zan je na tuntubi manya na, wadanda dama su ne suka zauna, suka yanke shawarar cewa na fito takarar nan. Daga nan kuma sai na yanke kuma na cimma matsayar da zan dauka.

“Tunda jam’iyya ta dauki matsayar ta, ni kuma zan jira hukuncin da Allah zai yanke nan gaba kadan.

“Domin dai abin da Dokar Kasa ta ce a yi kuma a dauka, ba shi aka bi ba, wajen fidda wanda zai zama shugaban majalisar dattawa. Majalisa ce za ta nada shugaba da mataimaki, ba jam’iyya ko wasu ’yan-kakuduba ba.

“Tunda sai da manyan mu suka shawarta, sannan suka nemi na fito, kuma su ma wasu sanatoci suka mara min baya, sannan kuma ita kan ta jam’iyyar ba ta kai ga cewa ta zabi Ahmed Lawan din ba tukunna. Cewa dai kawai ta yi ta amince da Ahmed Lawan.

WANDA YA NADA AHMED LAWAN YA NADA WA TUKUNYA RAWANI

“Tsarin da doka ta ce a bi domin fitar da Shugaban Majalisa, ya na nan dalla-dalla a cikin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya. Don haka duk wata hanya da za a bi a nada wani, idan ba ita aka bi ba, nadin haramtacce ne, ba zai dore ba.

“Wannan yakin fa ba ni kadai ba ne na daura shi, shawarta ta aka yi aka ce na fito takara, ni kuma na amince. Ai ni kadai kankin kai na ba zan bugi kirji don ina Sanata haka kawai na ce zan nemi shugabancin majalisa ba. Sai na samu goyon baya.

“A yanzu dai ba zan kai ga cewa an rigaya an kakaba mana shugaban majalisa ba. wuka da nama ya na a hannun mu ‘yan majalisar.

“Duk wanda zai waiwaya baya, to zai iya hango cewa irin wannan dauki-dorar da aka yi a baya ai ba ta taba dorewa ba.

“Cikin 1999 an kakaba Evan Ewerem. Bai dore ba, aka yi masa ‘korar-kare’. Aka dora Alphonsus Wabara, shi ma bai yi nisa ba. daga nan ai PDP din da mu ke zagi na ta yin karfa-karfa, ba ta sake yin irin haka din ba.

“Kun ga a cikin 2007, sai PDP ta koyi darasi, ta maida zaben shugaban majalisar ga Arewa ta Tsakiya, a karkashin tsarin karba-karba. Wannan ce ta sa aka yi takara a tsakanin David Mark da George Akume, inda Mark ya yi nasara.

“David Mark ya yi zango biyu, da kuwa PDP ta sake yin nasara a zaben 2015, to zai iya yin zango na uku.

ME YA SA AKE GUDUN AHMED LAWAN

A siyasar Najeriya kuma a cikin APC, da daman a yi wa Sanata Ahmed Lawan kallon yaron Bola Tinubu. Wasu na kaffa-kaffa da shi ne, domin sun a ganin idan ya zama Shugaban Majalisar Dattawa, to an kara wa Tinubu karfin siyasa ne.

Tinubu ke da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, kuma shi ne jagoran APC. Sannan kuma wani daga cikin yaron na sa, Hon. Femi Gbajabiamilla ake so a ba shugabancin Majalisar Tarayya.

ME ZAI IYA BIYO BAYA?

Idan APC ba ta sasanta wannan wutar rikici da ta fara ci ba, to jam’iyyar za ta iya shiga irin rikicin da ta shiga a baya.

A lura da cewa ana wannan rikicin a yanzu, daidai da har yanzu dai Sanata Bukola Saraki ne Shugaban Majalisar Dattawa tukunna.

Sannan kuma shi Saraki ne ya kayar da Ahmed Lawan a 2015, bayan da APC ta ce ita Ahmed din ta ke so ya zama shugaba.

A KULA: Ndume zai iya zama Shugaban Majalisar Dattawa, ko da babu amincewar APC da shugaban kasa. Abin da kawai zai yi shi ne, shi da dukkan sanatoci masu goyon bayan sa daga bangaren APC, za su hada kai ne da sanatoci na bangaren PDP su mara masa baya.

Ta yaya haka zai yiwu? Abu ne mai sauki. APC na da sanatoci 65, Ita kuma PDP 43. To idan masu goyon bayan Ndume daga APC suka hade da 43 na PDP, shikenan, aikin Gama ya Gama, kamar yadda aka gama da PDP a Mazabar Gama ta Kano.

Share.

game da Author