Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayyana cewa wasu mutane 23 sun kamu da Zazzabin Lassa a kasar nan.
Shugaban hukumar Chikwe Ihekweazu ya sanar da haka inda ya kara da cewa hukumar ta gano haka ne daga jihohi tara wanda suka hada da Edo, Ondo, Ebonyi, Bauchi, Taraba, Imo, Enugu, Benuwai da Kebbi.
Ihekweazu ya kuma ce daga cikin mutane 23 din mutane hudu sun mutu a jihohi uku da suka hada da Edo, Benue da Bauchi.
Ya ce daga cikin mutane uku din da aka rasa mutum daya ma’aikacin kiwon lafiya ne daga jihar Ebonyi.
Bayan haka Ihekweazu yace daga watan Janairu zuwa Maris mutane 495 ne suka kamu da zazzabin Lassa inda daga ciki 114 suka rasa rayukan su a jihohi 21 a kasar nan.
Jihohin da cutar ta bullo sun hada da Edo, Ondo, Bauchi, Nasarawa, Ebonyi, Plateau, Taraba, FCT, Adamawa, Gombe, Kaduna, Kwara, Benue, Rivers, Kogi, Enugu, Imo, Delta, Oyo, Kebbi da Cross River.
Ya kuma ce adadin yawan ma’aikatan kiwon lafiyan da suka kamu da wannan cutar bana sun kai 16 daga jihohi bakwai.
Wadannan jihohi sun hada da Edo, Ondo, Ebonyi, Enugu, Rivers, Bauchi da Benuwe.
Ya ce mutanen da suka yi mu’amula da wadanda suka kamuwa da cutar 2353 na samun kula a asibitocin kula da masu dauke da cutar a kasar na sannan an salami mutane 3384 kuma.
Hanyoyin gujewa kamuwa da zazzabin Lassa:
1. Da zaran mutum ya kamu da zazzabi a tuntubi likita domin tabbatar da cutar da mutum ke dauke da shi.
2. Duk ma’aikacin kiwon lafiya da zai duba mara lafiya a asibiti ya tabbata yana sanye da safar hannu sannnan ya kuma tabbata ya wanke hannayen sa da kyau bayan ya gama duba mara lafiya.
3. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbatar sun nemi magani da zarar alluran da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.
4. A tabbata an tsaftace muhalli da kuma adana kayan abinci nesa da fitsari da kuma kashin beraye.
5. Ba a iya kamuwa da cutar zazzabin Lassa idan an taba wanda ke dauke da cutar amma za a iya kamuwa da shi idan
Discussion about this post