Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta bayyana cewa an yi garkuwa da wani dan kasar Koriya ta Kudu, mai suna Jeng Sunail.
Cikin wata takardar sanarwa da Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Zamfara, Mohammed Shehu ya fitar ga manema labarai jiya Talata, ya ce ana tunanin an yi garkuwa da shi ne a Karamar Hukumar Tsafe.
Sunail, wanda likita ne, wani abokin aikin sa mai suna Li Dong ne ya kai rahton bacewar sa a Ofishin ‘Yan sanda na Tsafe.
An kai rahoton bacewar Jang Sunail wanda suka ce ya na zaune ne a wani gida tare da wasu abokan aikin sa su uku.
Shehu ya ce Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Celestine Okoye ya tura gagarimar tawagar jami’an tsaro domin fara bincike da kuma nema da ceto Sunail.
Wani da aka sace Sunail a gaban sa, mai suna Mustapaha Magazu, ya shaida wa manema labarai cewa wasu mahara ne suka dira garin da karfe 9 na dare, a ranar Litinin.
Ya ce ba su zame ko in aba sai gidan su Sunail, kuma kai-tsaye suka zarce dakin da ya ke kwana, suka yi awon-gaba da shi.
Wanda aka sace din dai gwamnatin jIhar Zamfara ce ta dauke shi aikin likita a Babban Asibitin Tsafe.