Kungiyar Kwadago bata amince da naira 27,000 a matsayin mafi karancin Albashi ba

0

Sakataren Kungiyar Kwadago Peter Ozo-Eson ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa kungiyar ba za ta amince da karin karancin albashi kasa da naira 30,000.

Ya ce amincewa da kwamitin kasa ta yi na naira 27,000, ba da yawun kungiyar bane saboda haka musu can, ” Mu dai naira 30,000 ne muka tsaya kuma ba za mu yadda da wani abu kasa da haka ba.

” Abin da muke so gwamnati ta yi tun ba yanzu ba shine ta mika kudirin mu ga majalisar dokoki ta kasa domin a fara tattaunawa amma taki.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne kakakin Yada Labaran Shugaba Muhammadu Buhari, Femi Adesina, ya bayyana cewa biyan ma’aikatan gwamnati naira 30,000 a matsayin mafi kankantar albashi, ba abu ne da zai yiwu ba a yanzu a kasar nan.

Tun farko dai kungiyoyin kwadago sun nemi a maida mafi kankantar albashi ya zama naira 50,000, amma daga baya kungiyar ta kafe a kan naira 30,000.

Kungiyar kuma ta ki karbar tayin da Gwamnatin Tarayya ta yi mata na kara mafi karancin albashin daga naira 18,000 zuwa naira 24,000.

A kan haka ne kungiyar ta ce za ta tafi yajin aiki a ranar 6 Ga Nuwamba.

Sai dai kuma da ya ke magana a Gidan Talbijin na Channels, a jiya Alhamis, Kakakin Buhari, Adesina, ya ce wasu gwamnoni da dama fa ba su ma iya biyan naira 18,000 a matsayin mafi karancin albashi, ba ma ta maganar karin albashin zuwa naira 30,000 ba.

“Don haka idan har ba su iya biyan naira 18,000, sannan kuma a yanzu kungiyar kwadago na neman a maida shi zuwa naira 30,000, za a iya samun tsaiko wanda ba zai yi wa kasar nan dadi ba.

“Ni ina ganin cewa kungiyar kwadago ta dan sassauta, kada ta jajirce ta ce sai karin ya kai naira 30,000 a bisa tilas.” Inji Adesina.

An tambaye shi idan har shugabannin siyasa musamman na jam’iyyar APC da ke mulki a yanzu suka rage albashin su, ko jihohi za su iya biyan albashin? Sai ya ce ba ya tsammani za su iya biya.

“ Ai ko da shugabanni da masu rike da manyan mukamai a gwamnati sun ce ba za su karbi albashi dungurugum ba, hakan ba zai sa a iya biyan naira 30,000 a matsayin mafi kankantar albashi a kasar nan ba.

“ Mai yiwuwa idan ‘yan majalsar tarayya suka zabtare albashi da kudaden alawus din su, to za a iya samun dan kari kadan kyas na mafi kankantar albashi. Amma sauran masu rike da mukamai dan abin da ake biyan su bai taka kara ya karya ba.”
Inji shi.

Kakakin Yada Labaran Shugaba Muhammadu Buhari, Femi Adesina, ya bayyana cewa biyan ma’aikatan gwamnati naira 30,000 a matsayin mafi kankantar albashi, ba abu ne da zai yiwu ba a yanzu a kasar nan.

Tun farko dai kungiyoyin kwadago sun nemi a maida mafi kankantar albashi ya zama naira 50,000, amma daga baya kungiyar ta kafe a kan naira 30,000.

Kungiyar kuma ta ki karbar tayin da Gwamnatin Tarayya ta yi mata na kara mafi karancin albashin daga naira 18,000 zuwa naira 24,000.

A kan haka ne kungiyar ta ce za ta tafi yajin aiki a ranar 6 Ga Nuwamba.

Sai dai kuma da ya ke magana a Gidan Talbijin na Channels, a jiya Alhamis, Kakakin Buhari, Adesina, ya ce wasu gwamnoni da dama fa ba su ma iya biyan naira 18,000 a matsayin mafi karancin albashi, ba ma ta maganar karin albashin zuwa naira 30,000 ba.

“Don haka idan har ba su iya biyan naira 18,000, sannan kuma a yanzu kungiyar kwadago na neman a maida shi zuwa naira 30,000, za a iya samun tsaiko wanda ba zai yi wa kasar nan dadi ba.

“Ni ina ganin cewa kungiyar kwadago ta dan sassauta, kada ta jajirce ta ce sai karin ya kai naira 30,000 a bisa tilas.” Inji Adesina.

An tambaye shi idan har shugabannin siyasa musamman na jam’iyyar APC da ke mulki a yanzu suka rage albashin su, ko jihohi za su iya biyan albashin? Sai ya ce ba ya tsammani za su iya biya.

“Ai ko da shugabanni da masu rike da manyan mukamai a gwamnati sun ce ba za su karbi albashi dungurugum ba, hakan ba zai sa a iya biyan naira 30,000 a matsayin mafi kankantar albashi a kasar nan ba.

“Mai yiwuwa idan ‘yan majalisar tarayya suka zabtare albashi da kudaden alawus din su, to za a iya samun dan kari kadan kyas na mafi kankantar albashi. Amma sauran masu rike da mukamai dan abin da ake biyan su bai taka kara ya karya ba.” Inji shi.sai ta buge da tattauna batun a taron majalisar Kasa da basu da hurumin yanke wa ma;aikata karancin albashin da ya kamata a biya su.

Share.

game da Author