Lauyar shugaban kungiyar Shiite, IMN, Ibrahim El-Zakzaky, na cikin matsannancin hali na fama da idon sa daya da ya rage bayan dama dayan ta daina aiki tun bayan arangamar kungiyar sa da sojojin Najeriya.
Wannan sune kalaman da babban lauyan da ke kare sheikh Ibrahim El-Zakzaky a kotu a garin Kaduna, Femi Falana ya yi bayan zama da ta yi don ci gaba da sauraren shari’ar da ke yi tsakanin sa da gwamnatin jihar Kaduna.
Falana ya ce ita kan ta matar sa, Zeenatudden da ke tsare na fama da radadin raguwar burbudin harshashi da ba a iya an cire duka a jikin ta ba.
Daga nan sai yayi kira ga likitocin gwamnati da na El-Zakzaky da su hada kai su bada shawara a fitar dashi zuwa kasashen waje don neman magani.