INEC ta maida wa Obasanjo martani: ‘Babu wani mai tirsasa mu yin ba daidai ba’

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta maida wa tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo martanin cewa babu wani mai tirsasa hukumar ko wani jami’ain ta su yi ba daidai ba.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne da kan sa ya maida wannan martanin a ranar litinin, ya na mai cewa zargin da Obasanjo ya yi kwata-kwata ba gaskiya ba ne.

Yakubu ya yi wannan karin haske ne a lokacin da ya ke jawabi a taron ganawa da ya yi da Sabon Sufeto Janar na ‘Yan sanda, Mohammed Adamu da wasu manyan jami’an ‘yan sanda jiya Litinin a Abuja.

Ya ce dama tunda lokacin zabe ya gabato, za a rika jin irin wadannan kalamai na bata wa INEC suna da sauran zarge-zarge marasa tushe balle makama.

“Amma dai ina kara tabbatar muku da cewa mu a wannan hukuma ba wani mai tirsasa mu ya ce sai mun yi ba daidai ba.

“Mu ba za mu taba sayar da gaskiyar mu ko mu bari kima da mutuncin mu ya zube kasa ba. Ba za mu taba yin abin da doka ba ta ce mu yi ba.

“Ganin yadda mu ke da irin wannan goyon baya daga jami’an tsaro, ina tabbatar muku da cewa za a yi zaben 2019 lami-lafiya cikin kwanciyar hankalil.

Ya kara da cewa kasar nan an zuba wa INEC da rundunar ‘yan sanda ido domin su tabbatar sun gudanar da sahihin zabe ingantacce.

Ya kuma ce za a bai wa kafafen yada labarai damar samun dukkan bayanan da suke nema a lokacin zabe.

Yakubu ya nemi karin hadin kan jami’an tsaro wajen gurfanr da wadanda ake kamawa da karya dokokin zabe.

Za a gudanar da zaben shugaban kasa da na majalisar dattijai da ta tarayya a ranar 16 Ga Fabrairu, shi kuma na gwamna da na majalisar jihohi a ranar 2 Ga Maris.

Share.

game da Author