Rashin ganin wulkawar gwamnonin jihohin da jam’iyyar APC a taron kwamitin kaddamar da Kamfen din Buhari da aka yi a dakin taro dake fadar shugaban kasa ranar Alhamis ya sa da dama ana ta dan rage murya a tsakanin wasu ‘ya’yan jam’iyyar da suka halarci taron.
Idan ba a manta ba shugaba Buhari ya bayyana cewa a kamfen din sa, tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu ne wuka, shine nama wajen shirya kamfen din da wasu hidindimu da za a gudanar a lokacin kamfen din sa.
Kazalika, Buhari ya kara da yin kira ga mutanen Najeriya da kada su zabi gwamnonin da suka kasa biyan su albashi da wasu hakkokin su duk da dama da suka samu na
Wasu na ganin hakan na daga cikin dalilan da ya sa kila wasunsu suka kaurace wa taron a yau Alhamis.
Buhari zai ziyarci Kaduna, Bauchi da Gombe a karshen wannan mako da muke ciki.