Karatu ko wanne iri ne, amfaninsa shine ayi aiki dashi wajen samar wa da kai mafita. Kamar yadda na taba fada a wata jarida, duk irin abun da ka karanta zaka iya samar wa da kanka sana’a dashi.
Mafi saukin abun da zaka iya farawa shine siyar da ilimin da kake dashi, tunda shima kyakykyawar haja ce ta siyarwa (Knowledge is a commodity for sale in this postmodern world).
Mu a Afrika ne ma ake yin karatu saboda ayi aikin gwamnati shiyasa zaka samu wanda ya kammala Digiri’graduate’ ya kai shekara goma (10 years) yana ta neman aiki bai samu ba. Kuma ya sakawa zuciyarsa cewa idan ba aikin gwamnati ba sai rijiya.
Dole kuwa a sha wahala tunda su masu bayar da aikin ba zasu baka ba saboda rashin aikin ko hassada ko son zuciya. Wannan maganar inaso duk wani matashi yayi nazari akanta.
A matsayinka na matashi kana da lokacin tunani akan mai yakamata ka yiwa rayuwarka saboda ka gina tsufanka kafin yazo. Yanzu ne muke da karfi da lafiyar da zamu iya gina rayuwar mu dasu.
Ajje takardar NCE ko HND ko BSc ko MSc dinka a gefe ka Kirkirowa mutane alheri, iliminka shine abokin aikin ka, ba wai tsurar takardar da aka baka a makaranta ba. Duk sanda ka gwada yin haka, insha Allah zaka dace, zaka samu farin ciki a matsayinka na wanda ya kirkiro alherin da mutane suke amfana.
Mai karatu kasan cewa wasu ‘yan uwan naka da abokan arziki suna da damar da zasu sama maka aiki amma jari-hujja ya hanasu? Kuma zaka yi mamaki idan ka gina tafiyarka tayi kyau duk zasu dawo jikin ka. To daure ka fara ginin tun yanzu.
Lomar tuwo tana da mahimmanci a rayuwa. Karl Marx yace, bukatar mutum ta farko itace abinci saboda haka ne ma yake shiga cikin harkalla da mutane don ya cika burinsa na abun da zai ci. Hakazalika, wani masanin bukatun ‘dan adam mai suna Abraham Maslow yace, a cikin “hierarchy of needs” abinci yana cikin bukatu na farko.
Na kawo wadannan maganganun ne saboda na samar wa maganata hujja a duniyar ilimi. Tabbas, duk abun da zamu yi muna da bukatar lomar tuwo shiyasa nake bawa ko wanne ‘graduate’ shawara da ya cire burin samun aikin gwaunati a gefe saboda ya samar wa da kansa aiki har ya bawa wasu.
Misali, na karanta kimiyar siyasa amma tun kafin na gama karatun ina da abun yi, bayan na gama sai na kara inganta sana’a ta saboda bani da lokacin da zan dinga bin ofisoshin mutane neman aiki suna bata min lokaci a wannan duniya ta jari-hujja.
Na fara ne tun daga karamar sana’a, kafin daga baya na fara siyar da ilimi na, wanda a yanzu babu abun da zan cewa Allah sai godiya.
Duk da nasan fara wa yana da wahala amma a Kashin gaskiya babu abun da ya kai farawar amfani saboda ba zaka san kai wane iri bane sai ka shiga cikin gwagwarmayar neman lomar tuwo. Bahaushe yace, na zaune bai ga gari ba.
Allah ya shiryar damu.