ZABEN 2019: Ba zan yi kamfen da kudin gwamnati ba – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba zai yi kamfen da kudin gwamnati domin a sake zaben sa ba.

Da ya ke magana lokacin rufe taron Majalisar Zartaswa a jiya Laraba, Buhari ya ce kada wani minista ya kwashi kudin gwamnati ya yi kamfen.

Maimakon haka, Buhari ya ce su yi amfani da kafafen sadarwa na zamani, musamman sakon text na wayar selula su na tura ayyukan ci gaban da gwamnatin APC ta gudanar domin jama’a su gani.

Haka kakakin sa Garba Shehu ya bayyana bayan kammala taron.

“Ba mu da kudin da za mu yi kamfen da su a asusun gwamnati. Saboda ba zan bada umarnin a yi haka ba.” Inji Buhari.

Buhari ya ci gaba da cewa ‘yan Najeriya na bukatar canji, kuma gwamnatin APC ce kadai za ta iya kawo wannan canjin.

Ya na mai karawa da cewa ‘yan Najeriya ba za su sake komawa a turbar siyasar wandaka da kudi ba.
Ya yi amfani da lokacin ya taya Karamar Ministar Harkokin Waje, Khadiza Ibrahim fatan alheri.

Khadiza ta ajiye aiki jiya Laraba, saboda ta shiga takarar majalisar tarayya.

Share.

game da Author