GARGADI: Kada ku zabi gwamnonin da suka ki biyan ku albashi, suka ki yi muku aiki – Inji Buhari

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga talakawan Najeriya da zabi gwamnonin da suka yi na’am da ayyukan su ne a tsawon mulkin su musamman irin wadanda suka kasa biyan su hakkokin su da ya hada da albashi da sauran su.

Buhari wanda shine dan takarar jam’iyyar APC a zaben shugaban kasa mai zuwa ya gargadi talakawa da su tabbata sun yi tankade da rairaya wajen zaben gwamnoni, su tabbata sun duba cancanta da kuma irin ayyukan da suka yi don ci gaban talakawar su.

Shugaba Buhari ya kara da cewa bai ga dalilin da zai sa gwamnatin tarayya ta ba gwamnoni kudi domin gudanar da ayyuka amma su gagara biyan albashin ma’aikatan jihohin su ba.

Buhari yace yana mamakin yadda irin wadannan gwamnoni kan iya kwantawa har su yi barci bayan sun san akwai mutanen dake aikin gwamnati basu biya su albashin su ba, sanin suna da gidaje, suna da iyali, basu biya kudin haya ba, basu biya bukatun iyalansu ba, da suka hada da biyan kudin makaranta, da zuwa asibiti da sayen abinci.

Shugaba Buhari yace tsarin dokar Najeriya ya ba gwamnonin ‘yancin kashe kudaden da suka samu ba tare da tsangwama ba, sai dai wannan ya zama damar da wadansu suke fakewa suna kin yi wa talakawa aiki.

A dalilin haka Buhari ya shawarci talakawa su yi amfani da ‘yancin su na zabe su zabi wadanda suka san zasu yi masu aiki.

Kamar yadda sashen Hausa na VOA suka ruwaito, da aka tambayi shugaba Buhari game da batun yaki da cin hanci da rashawa, shugaba Buhari yace hanyar da yake bi a halin yanzu ita ce hanyar da tsarin dimokradiya ya amince da shi.

Yace a baya ya dauki wani mataki na
dabam, amma kasancewa yanzu ana mulkin dimokradiyya ne tilas yabi tsarin. Sai dai yace duk da yake tsarin yana daukar lokaci, duk da haka, ana samun nasarorin gaske a abin da akasa a gaba.

Share.

game da Author