Jam’iyyar PDP ta dakatar da mataimakin jam’iyyar na kasa, na Arewa, Babayo Gamawa, saboda zargin sa da yin sakaci da aiki da kuma yi wa jam’iyyar yankan-baya.
Sakataren Yada Labarai na Kasa na PDP, Kola Ologbondiyan ne ya bayyana cewa Babban Kwamitin Zartaswa na PDP ne ya dakatar da Gamawa.
Kwamitin ya yi taron gaggawa ne a ranar 5 Ga Janairu, inda aka tattauna korafe-korafen da aka rika gabatarwa a kan Gamawa.
An samu rahotannin ficewar wasu daga PDP zuwa APC a Kano.
Discussion about this post