Boko Haram: Gwamna Shettima ya barke da kuka yayin ganawa da Buhari

0

Gwamna Kashim Shettima na Jihar Barno ya barke da kuka a gaban Shugaba Muhammadu Buhari, dangane da sake kwararowar Boko Haram bagatatan a jihar sa.

Kashim ya barke da kukan ne a lokacin da ya jagoranci wata tawagar manyan jihar da suka kai wa Buhari ziyara a Fadar Shugaban Kasa, Abuja yau Litinin.

Ya zuwa lokacin da ake runuta wannan labari, su na ci gaba da taron ganawar.

Gwamnan ya barke da kuka a lokacin da ya ke karanta jawabin dalilin sake zuwan su ziyara wurin shugaba Buhari.

Dukkan sanatocin jihar Barno su na wurin taron tare da mambobin majalisar tarayya na jihar da kuma dan takarar APC na gwamnan Barno da kuma sarakunan gargajiya.

Akwai kuma manyan shugabannin hukumomin tsaro a wurin taron.

Share.

game da Author