Kotun Koli ce kadai za ta iya tsige zababbun ’yan siyasa – Majalisar Tarayya

0

Ranar Laraba ce Majalisar Tarayya suka mika kudirin sun a yi wa Dokar Zabe ta Kasa Kwaskwarima, tare da cewa Kotun Koli ce kadai za ta iya tabbatar da soke zababben dan siyasa idan wata kotu ta tsige shi.

Majalisar Tarayya ta ce duk wani zababben dan siyasa da kotun sauraren kararrakin ko daukaka kara ta tsige, zai ci gaba da zama a kan mukamin sa ya na karbar dukkan hakkokin sa, har sai ranar da Kotun Koli ta tabbatar da cancantar tsigewar da aka yi masa.

Wannan sabon kudiri da Majalisar Tarayya ta amince da shi, ya na nan kunshe a cikin Sashe na 143 na kundin dokar zabe da ta yi wa kwaskwarima.

Sauran batutuwan da ke cikin kundin da aka yi wa kwaskwarima din, sun hada da batun yin amfani da na’ura mai kwakwalwar tantance katin shaidar zabe, wato ‘card reader’ da sauran na’urorin da aka amince a yi amfani da su a lokacin gudanar da zabe.

Akwai kuma batun iyar wa’adin lokacin mika sunayen ‘yan takara, matakan sauya dan takara da kuma takaita adadin kudaden da kowace jam’iyya ko dan takara zai kashe a lokacin kamfen.

Har ila yau kuma kudirin ya tabo batun cire sunan dan takara a bisa kuskure a jerin sunayen takardar kada kuri’a ko kuma rashin buga tambarin wata jam’iyya a cikin jerin sunayen jam’iyyun da suka fito takara.

Kudirin kuma ya rattaba a Sashe na 140 cewa duk wani jami’in hukumar zabe da ya cire sunan jam’iyya, na dan takara ko tambarin jam’iyya a takarar kada kuri’a, har abin ya yi sanadiyyar soke zaben ko daga zaben, to hukuncin daurin shekara biyu ko tarar naira milyan 2 ya hau kan sa.
Duk yawancin wadannan kudirorin an amince da su a Majalisar Dattawa.

Bayan Majalisar Tarayya ta amince da kudirin, sai ta umarci Magatakardan Majalisar Tarayya da ya mika Kudirin zuwa Fadar Shugaban Kasa, domin ya sa masa hannun amincewa.

Kudirin dai ba zai zama doka ba har sai Shugaba Buhari ya rattaba hannun amincewa a kan sa tukunna.

Share.

game da Author