Cikin Kudirin Dokar Zabe wanda Majalisar Tarayya ta amince da shi jiya Labara, kuma har ta umarci Magatakardar Majalisa ya mika wa Fadar Shugaban Kasa domin ya sa hannun tabbatar da shi ya zama doka, majalisar ta amince da adadin da jam’iyya ko ‘yan takara za su kashe a kokarin su na neman mukaman siyasa.
SHUGABANCIN KASA: Majalisar Tarayya ta amince dan takarar shugabancin kasa kada ya kashe abin da ya wuce naira biliyan 5.
TAKARAR GWAMNA: Dan takarar gwamna kada ya kashe abin da ya haura naira biliyan 1.
TAKARAR SANATA: Kada dan takarar Majalisar Dattawa, wato sanata ya kashe sama da naira miliyan 500.
MAJALISAR TARAYYA: Kada dan takarar Majalisar Tarayya ya kashe sama da naira miliyan 250.
MAJALISAR DOKOKI: Kada dan takarar zaben Majalisar Dokoki ta Jiha ya kashe sama da naira miliyan 50.
KARAMAR HUKUMA: Ba a yarda dan takarar shugabancin karamar hukuma ya kashe sama da naira miliyan 30 ba.
TAKARAR KANSILA: Kada dan takarar kansila ya kashe sama da naira miliyan 15.
ADADIN GUDUMMAWA: Kada gudummawa daga wani mutum ko wata kungiya ta zarta ya bayar da sama da naira milyan 10 ga jam’iyyar da zai bai wa gudummawar.