Mawallafin jaridar Daily Nigerian, Ja’afar Ja’afar ya bayyana wa kwamitin majalisar dokokin jihar Kano dake binciken badakalar karbar cin hanci karara da gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya rika yi cewa bidiyon da ya saki wa duniya don tona wa gwamnan asiri nagartacciya ce.
Idan ba a manta ba jaridar Daily Nigerian ta saki wani bidiyo dake nuna gwamnan jihar Kano, Ganduje, yana karkacewa ya na loda daloli a aljuhunsa daga hannun wani dan kwangila.
Ja’afar ya bayyana wa kwamitin dake zama a Kano yau, Alhamis cewa ya dade yana bibiyar gwamnan tun bayan da abokin sa da yake dan kwangila ne ya sanar masa da yadda gwamnan ya rika karbar cin hancin kashi 15-25 bisa 100 na duk kwangilan da ya bada a jihar Kano.
” Bayan nan sai na nemi shi dan kwangilan ya saka na’urar daukan hoto a jikin rigar sa. Mun dauke sa sama da bidiyo dabam dabam har kala 10 wanda kusan duka suna nuna fuskarsa da yadda yake ta karkacewa ya zura bandir-bandir din daloli a aljihun sa.
Ja’afar ya kara da cewa kafin ya wallafa sai da shahararrun gidajen jaridu kamar su PREMIUM TIMES, BBC suka tabbatar da nagartar wannan bidiyo sannan shi kan sa dake da mallakin bidiyon ya tabbatar da sahihancin sa run kafin wani ma ya san da haka.
Ya fadi wa kwamitin cewa zai mika musu wannan bidiyo wanda ma ba a taba ba su gani wa kan su. Sannan ya ce bayan haka ma zai mika wa ‘yan majalisan wasu bayanai da suka shafi wannan harkalla na gwamna Ganduje.
A yau Alhamis kungiyar Amnesty ta yi kira ga hukumomin tsaro da su tabbata ja’afar ya samu cikakkiyar kariya ganin cewa tun bayan da ya fallasa wannan badakala yake ta samun barazana a rayuwar sa.
Discussion about this post