Kakakin majalisar Wakilai Yakubu Dogara ya sayi fom din takarar Majalisar wakilai amma fa a jam’iyyar PDP.
Ko da yake Dogara bai maido kirar da PREMIUM TIMES ta yi masa ba domin tabbatar da wannan al’amari wani jigo a jam’iyyar PDP ya shaida mana cewa tabbas Dogara ya sayi fom din a jam’iyyar PDP kuma yanzu haka da ake ciki ana cika fom din.
“ Ina so in tabbatar muka cewa yanzu haka ana cika fom din, kuma da zarar an kammala za a mika wa jam’iyya. Gobe ne za a mika fom din.
Wani shima da ya tabbatar mana da haka ya ce kakakin majalisar ya sayi fom din takarar majalisar a ofishin PDP dake Abuja.
Duk da cewa bai bayyana ko ya fice daga jam’iyyar APC ba, tuni an riga an tabbatar da zarar an dawo daga hutun majalisa zai bayyana haka kamar yadda shugaban majlisar dattawa ya bayyana ficewar sa daga APC din.
Wasu mambobin majalisar da dama sun fice daga APC tun kafin majalisar ta tafi hutu a wancan lokaci.
Yanzu dai ko Dogara zai sha idan an dawo? Toh sai dai mu jira lokaci.