Za a horas da sabbin sojoji a dajin Falgore

0

Makarantar horas da sabbin sojoji dake Zariya Jihar Kaduna ta sanar cewa a daga ranar 17 zuwa 30 ga watan Satumba za a fara atisayin koyan harbi ga sabbin sojojin da aka dauka.

Jami’in makarantar Adekule Adeyemi –Akinyele ya sanar da haka ranar Laraba a Zariya sannan ya kara da cewa za su fara horon mai taken ‘Exercise Kungama’ a dajin Falgore dake hanyar Tudun-Wadan Saminaka

Akinyele ya bayyana cewa sun yi wannan sanarwa ne saboda mazaunan kauyen Falgore, Tudun-Wada, Kwanar Dan Gora da Dakatsalle su sani kada suji harbe-harbe su tsorata.

Ya kuma ce sanarwar ya yi kira ga mazauna kusa da wadannan garuruwa da su nisanta kan su da ga kusantar wannan daji domin za ayi amfani da manya-manyan bindigogi ne da tankunan yaki.

Share.

game da Author