Tsohon ministan Yada labarai Labaran Maku ya fito don sake fafatawa a yakin neman kujerar gwamnan jihar Nasarawa a 2019.
Kwamitin amintattu na jam’iyyar APGA ne ta amince da takarar Maku inda ta bashi tuta a yau Laraba.
Idan ba a manta ba Labaran Maku ya fara neman takarar gwamnan jihar Nasarawa ne tun a 2015 inda ya canza sheka daga PDP zuwa APGA bayan ya rasa tikitin takarar a PDP.
Darektan yada labaran Maku, Nawani Aboki, ya bayyana cewa tuni har an fara tuntubar juna game da wanda za a tsayar yayi masa mataimaki.
Discussion about this post