Da wakilai za mu yi zaben fidda dan takara a Kaduna – Jam’iyyar APC a Kaduna

0

A wani abu kamar sacce wa sanata Shehu Sani da wasu gaggan ‘yan siyasa da suka bukaci jam’iyyar APC ta amince da yin zaben fidda ‘yan takara ta hanyar ‘Kai tsaye’ wato (Direct), a yau Alhamis jam’iyyar A Kaduna ta sanar da amincewa da yin zaben ta hanyar yin amfani da Wakilai.

A sanarwa da shugaban jam’iyyar Emmanuel Jekada ya saka wa hannu a Kaduna, jam’iyyar tace ta hanyar yin zabe na wakilai ne za ta yi amfani da shi.

Jekada ya bayyana wasu dalilai da ya sa jam’iyyar ta dauki matsayin yin amfani da (Indirect) wato zaben da wakilai.

“ Mun gwada yin amfani da zabe na kai tsaye wato na bai daya a zaben fidda ‘yan takara lokacin da muke zaben kananan hukumomi a jihar. Hakan ya jawo tashin hankali matuka a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.

“ Bayan haka mu zabe na (Kai tsaye) na da matukar tsada. Sannan ko ta wajen daukar dawainiyar jami’an tsaro kawai za a jigata.

Ya ce uwar jam’iyyar ta aikawa hedikwatar jam’iyyar na kasa da matsayin ta.

Idan ba a manta ba, kusan duka jihohin da suka zabi salon yin zaben fidda dan takarar su sun yi na’am ne da fasali na zabe da wakilai.

Share.

game da Author