Adam Zango ya roki Ali Nuhu da ya yafe masa laifukan da yayi masa, yana mai cewa “Tuba nake Sarki, Guiwowi na a kasa” kamar yadda ya rubuta a shafin sa ta Instagram.
An dade ana ba a ga mai maciji tsakanin Adam Zango da Ali Nuhu a farfajiyar fina-finan Hausa.
Idan ba a manta ba babban dalilin fara samun matsala a tsakanin Ali Nuhu da Adam Zango ya samo asaline tun bayan rikici da ya kaure a tsakanin su da Rahama Sadau inda ta zarge sa da cire ta a fim din sa wai don ta ki amince masa ya kusance ta.
Daga baya, Rahama ta janye wannan Magana inda ta ta roki yafiya daga Zango.
Tun bayan wannan rikici, ba a sake samun daidaituwa tsakanin Zango da Ali ba. A kullum Zango yakan soki Ali da aikata wani laifi a kan sa. Sai dai Ali bai taba cewa komai ba kai.
A kwanakin baya sai da manya a farfajiyar suka shiga tsakani, sannan aka sake samun daidaituwa a tsakanin su.
A yanzu dai Adamu ya hakura ya durkusa wa Ali ya roki gafara.
Dubban masu bin Zango a shafin sa ta Instagram sun jinjina wa Zango kan kaskantar da kan sa da yayi ya roki yafiyar Ali.
Ali dai a matsayin sa na babba, bai ce komai ba a kai, kamar yadda ya saba.