A yau Alhamis ne shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da gwamnan jihar Benuwai Samuel Ortom suka ziyarci hedikwatar jam’iyyar PDP.
Idan ba a manta ba dukkan wadannan jiga-jigan ‘yan siyasa sun fice daga jam’iyyar APC ne.