Masu garkuwa sun yi garkuwa da fitaccen malamin nan mazaunin garin Kaduna Sheikh Ahmad Algarkawi a gonar sa dake Kaduna.
Wata ‘yar uwar malamin ta tabbatar wa PREMIUM TIMES aukuwar haka, inda ta bayyana cewa ta hanyar zuwa Gusau ne aka kira ta a ka gaya mata wannan mummunar al’amari.
Wani daliban sa Mal. Lawal shima ya tabbatar mana da aukuwar wannan al’amari. Ya fadi cewa malamin ya tafi gonar sa ne dake Unguwar Nariya tare da wasu daga cikin daliban sa da a nan ne suka gamu da masu garkuwan.
‘Yan sandan jihar Kaduna basu ce komai akai ba duk da neman haka da muka yi.