Tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Aliyu Magatakarda Wamakko ya bayyana cewa babu wai don gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal ya canza sheka zuwa jam’iyyar APC ba zai canza alkiblar siyasar jihar ba.
Wammako da yake amsa tambaya kan ficewar gwamnan jihar Aminu Tambuwal daga jam’iyyar APC a talabijin din NTA, da jaridar Daily Trust ta ruwaito, ya bayyana cewa babu wani abin da zai basu tsoro wai don gwamnan jihar ya koma PDP.
Wamakko ya ce APC ce a jihar Sokoto kuma ko shakka bau ita ce ke kan gaba a zukatan mutanen jihar.
Ya ce shi ba sa’ar gwamnan jihar Tambuwal bane, kuma zai nuna wa duniya cewa ya fi Tambuwal jama’a a jihar Sokoto, sannan jam’iyyar APC da Buhari ne kawai a ke yi a jihar Sokoto.
” A saurari shiga na garin Sokoto a karshen wannan mako.”
Discussion about this post