An canza wurin taron kaddamar da takarar Kwankwaso zuwa Otel din Chida

0

Kakakin tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso, Binta Sipikin, ta sanar cewa a dalilin kin amincewa Kwankwaso ya yi taron kaddamar da neman takarar shugaban kasar sa a dandalin Eagle Square, Kwamitin shirya kaddamarwar ta canza wurin taron zuwa Otel din Chida dake unguwar Utako, Abuja.

Idan ba a manta na kasa da awa 24 kafin lokacin da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Kwankwaso ya fito domin kaddamar da kan sa neman takarar shugabancin kasa, karkashin jam’iyyar PDP, hukumomi sun hana shi yin amfani da Dandalin ‘Eagle Square’, wanda tun da farko a can ne aka shirya za a gudanar da gangamin.

Haka kuma PREMIUM TIMES ta samu labarin cewa an hana Kwankwaso yin amfani da Tsohon Filin Faretin Abuja, da ke daura da Cibiyar Taro ta Kasa da Kasa.

Kwankwaso wanda kwanan nan ya fice daga APC ya koma PDP, ya sanar da cewa a gobe Laraba ne zai kaddamar da neman fitowa takarar shugabancin kasar nan a fafata da shi a karkashin jam’iyyar PDP.

Cikin wata wasika da manajan filin taro na ‘Eagle Square da International Conference Centre,’ mai suna Usman Raji ya sa wa hannu, ta ce an hana Kwankwaso gudanar da taron ne a Eagle Square, domin kada cinkoson jama’a ya hana ma’aikatan gwamnati zirga-zirga da gudanar da ayyukan su kamar yadda ya kamata.

Ya ce a nan ne Sakateriyar Gwamnatin Tarayya ta ke, inda nan ne dandazon rukunin ma’aikatun gwamnatin tarayya da kuma dubban ma’aikatan gwamnati suke.

Usman Raji ya ba su hakuri tare da cewa hakan ya faru ne saboda an aza ranar taron ne ta yi daidai da ranar aiki.

Sai dai Tawagar Kamfen din Kwankwaso ta ce wannan wata manakisa ce daga gwamnati saboda ba ta son duk wani ci gaba na dimokradiyya.

Sun shaida cewa tun kafin su shirya wannan taro a filin ‘Eagle Square’ sai da suka biya kudin da ke biya domin hayar wannan fili, sannan kuma ko a wancan lokaci ba a ce musu baza a basu ba.

” Kwatsam sai gashi yanzu an ce wai saboda tsaro da walwalan ma’aikatan gwamnati an hana mu wannan fili.”

Da muka nemi ji daga bakin ministan Abuja, kakakin sa ya ce minista Abubakar Bello ba shi da masaniya a kai.

Share.

game da Author