WHO za ta yi wa yara 15,000 allurar rigakafin cutar shawara a jihar Katsina

0

Jami’ar kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) Charity Warigon ta bayyana cewa kungiyar tayi hadin guiwa da kamfanin sarrafa magunguna GAVI don yi ya yara sama da 150,000 allurar rigakafin cutar shawara a karamar hukumar Danja, jihar Katsina.

Warigon ta fadi haka ne a shafin kungiyar na sada zumunta a yanar gizo sannan ta kara da cewa kamfanin GAVI za ta tallafa wa mata da maganin allurar rigakafi miliyan 12 a 2018 sannan ta karo wasu miliyan 19 don 2019.

Ta ce za su yi ya yara ‘yan watanni 9 zuwa masu shekaru 45 sannan allurar za ta kare mutum daga kamuwa da cutar har tsawon rayuwar sa.

Warigon ta bayyana cewa sun yi haka ne domin mara wa gwamnatin Najeriya baya wajen ganin ta cimma burin ta na inganta lafiyar mutanen kasar.

” Rahotan NCDC ya nuna cewa a shekarar 2017 cutar ta bullo a jihohi 11 a Najeriya sannan akalla mutane 2,400 sun kamu da cutar sannan mutane 47 sun rasa rayukan su a dalilin kamuwa da cutar.

A karshe Warigon ta ce a yanzu haka sun tallafawa jihohi 10 a Najeriya da alluran rigakafin cutar shawara sannan za su ci gaba da haka a jihohin Sokoto, Neja, Filato, Barno, Kebbi da Abuja.

” Za mu fara yin rigakafin ne a wadannan jihohin ranar 8 zuwa 17 ga watan Nuwamba.”

Share.

game da Author