Gwamnatin Kaduna ta umarci maso muradin fitowa takarar kujerun Majalisa su ajiye ayyukan su

0

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi kira ga jami’an gwamnati da ke muradin fitowa takarar kujerun majalisar jiha su mika takardun ajiye aikin su.

Kakakin gwamna Nasir El-Rufai ne ya bayyana haka a wata takarda da ya saka wa hannu ranar Talata.

Ya ce gwamnati ta yi haka ne domin bin dokar jam’iyya, domin haka ta shar’anta.

Share.

game da Author