Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da shugabannin rundunonin tsaron kasar nan a fadar sa ranar Litini.
Makasudin wannan ganawa kuwa shine domin a tattauna halin da ake ciki musamman abin da ya shafi tsaro a kasar nan da kuma yaki da Boko Haram da ake yi a yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya.
Shugaba Buhari ya hore su da su maida hankali matuka a aikin su sannan su tabbatar ana samun nasara a ayyukan tsaro da aka sa a gaba.
A Lahadin da ta gabata Boko Haram sun kai hari kauyen Mailari dake yankin Guzamala a jihar Barno inda akalla mutane 19 suka rasu a sanadiyyar wannan hari.
Sai dai wani ma’aikacin sansanin ‘yan gudun hijira da ke yanki da ba ya so a fadi sunan sa ya bayyana cewa a dalilin wannan hari mutane 63 ne suka rasa rayukan su.
Da ya ke tofa albarkacin bakin bayan ganawar, ministan tsaro Mansur Dan-Ali rundunonin tsaro na kasa za su ci gaba da yin aiki tukuru domin ganin an sami wanzuwar zaman lafiya a kasa Najeriya.
” Dakarun Najeriya suna kokarin gaske a musamman jihohin Zamfara, Benuwai, Kaduna da sauran sassan kasar nan, za a ci gaba maida hankali wajen ganin an kau da ayyukan masu tada zaune tsaye a fadin kasar nan.” Inji Dan-Ali.