‘Yan bindiga sun harbe wani limami sun sace matar sa a Kaduna

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta sanar cewa wasu ‘yan bindiga sun harbe wani limanin cocin Nasara Baptist mai suna Hosea Akuchi dake kauyen Guguwa a jihar Kaduna.

Kakakin rundunar Yakubu Sabo ya sanar da haka ranar Talata sannan ya kara da cewa akwai yiwuwar cewa ‘yan bindigan masu garkuwa da mutane ne domin sun sace matar limanin mai suna Talatu bayan harbe mijin ta.

Ya ce ‘yan bindigan sun shiga gidan limamin cocin ne dake karamar hukumar Igabi da karfe dayan dare.

“Akwai yiwuwar limamin ya dan yi gaddama da ‘yan bindigan ne da hakan ya sa suka harbe shi kafin suka tafi da matar sa”.Inji Sabo

Sabo yace har yanzu dai masu garkuwan basu ce komai ba game da kudin fansa sai dai sun riga sun fara bincike akai.

Ya ce aiyukkan mahara irin haka ya addabi mutanen jihar Kaduna xuk da kokarin dakile ayyukan nasu da gwamnatin jihar ta maida hankali a kai.

Share.

game da Author