A yau Talata ne masarautan Jema’a ta nada gwamnan jihar Kaduna Nasir El- Rufai sarautan Garkuwan Talakawan Jema’a.
Gwamna El-Rufai ya yi sallan Idi ne a garin Jema’a inda dubban magoya bayan gwamnatin jihar suka fito kwan su da kwarkawatan su domin yi masa lale-lale maraba da zuwa masarautar Jema’a.
Kakakin gwamnan jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a shafin sa na Facebook.
A cikin tawagar gwamna El-Rufai akwai mai ba gwamna shawara kan harkokin siyasa kuma dan takaran sanata na Kaduna ta Tsakiya, Mal Uba Sani.

