Ibikunle Daramola na rundunar sojin sama ya bayyana cewa mayakan su sun yi wa maboyar mahara da suka hana mutanen jihar Zamfara sakat a dazukan da ke zagaye garuruwan jihar.
Mutanen jihar Zamfara na fama da hare-haren ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane da hakan yaki ci yaki cinyewa. A dalilin haka ne gwamnati ta tura dakarun ta domin fatattakar wadannan mutane da ruguza shirin su da ayyukan su a fadin jihar.
Daramola ya ce dakarun ‘Operation Diran Mikiya’ sun rugurguza wurare da ‘yan ta’adda ke amfani dasu wajen kitsawa da shirya ayyuka ta’addanci a fadin jihar.
A karshe Daramola ya ce rundunar za ta ci gaba da sauraron muhimman bayanai daga mutanen gari domin samun nasara akan abin da ta sa a gaba.