Shugaban Kula da Masu Bautar Kasa(NYSC) na jihar Jigawa, Ibrahim Mohammed, ya bayyana cewa kashi 75 bisa 100 na ‘yan bautar kasar da ke cikin jahar duk an tura su yin aiki a Karkara ne.
Da ya ke magana a Dutse, ranar Litinin, a wurin bikin rufe horas da ‘yan Sansanin “B”, Ibrahim ya ce an tura su cikin karkara ne, saboda a can ne aka fi bukatar su.
Ya ce yawancin masu bautar kasar an tura su ne a makarantun sakandare da kuma cibiyoyin kula da lafiya, inda za su rika koyarwa kuma su a gudanar da ayyukan kula da lafiyar jama’a.
Daga nan sai ya yi kira da matasan da su girmama dabi’u da al’adun al’ummar da aka tura su cikin su, sannan kuma su yi kokari su koyi yaren su.
Ya kara gargadin su da su tabbatar da kiyaye dokokin hukumar NYSC da kyau.
Shi ma gwamnan Jihar, Muhammad Badaru, ya hore su da su zama masu ‘yan kasa nagari kuma masu da’a.
Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Adamu Finini ne ya wakilci gwamnan.