Wadanda suka fice daga APC duk ‘yan Kashe mu raba ne da ma can – Inji Oshiomhole

0

Shugaban jam’iyyar APC ya bayyana cewa ko kadan hankalin sa bai tashi jin wai wadansu ‘yan jam’iyyar sa sun fice daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.

” Ni fa babu abin da zai hanani barci har da minshari domin kuwa dama can ba kwaunar APC suke yi ba. Dukkan su yan kashe mu raba ne ba masu son ci gaban jam’iyyar APC ba.

” Dukkan su babu wanda Buhari bai ci mazabar sa ba, kuma wannan abin farin ciki ne domin gara da suka fice yanzu ma domin kunga za ma san yadda za mu tsara kamfen din mu domin tunkarar 2019.

” Kuma dama can duk da suna jam’iyyar APC, sun zamo mana kayan kifi a wuya, sai suka zama kamar bangaren adawa na jam’iyyar.

Idan ba a manta ba a safiyar Talata din nan ne sanatoci 15 suka koma jam’iyyar PDP sannan wasu ‘yan majalisar wakilai 34 suma suka koma jam’iyyar PDP din.

Share.

game da Author