Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, ya bayyana yadda ya zille wa kawanyar da jami’an ‘yan sanda suka yi wa gidan sa da nufin hana shi fita zuwa majalisa.
Ya ce duk da kewaye gidan sa da aka yi, hakan bai hana shi isa zauren majalisa da misalin karfe 10:40 na safe ba.
“Ni dama tuni tun jiya na kwana da shirin cewa hakan na iya faruwa. Don haka da shiri na na kwana.
“Mataimakin Shugaba, Ekweremadu ya kira ni ya ce min ba zai iya zuwa ba, saboda shi ma jami’an tsaro sun kewaye gidan sa.”
Sai dai kuma Ekweremadu ya isa majalisa bayan sha biyu na rana.
“Tun karfe 6:30 aka tare titin gida na, ba shiga kuma ba fita.
“An jera motoci na tun safe, amma aka hana kowane direba motsawa daga inda ya ke tsaye da mota.”
A karshe dai ya ce Allah ne ya kubutar da shi har ya kai kan sa majalisa, inda ya na zuwa ya shiga zauren zaman majalisa.
Dangane da abin da ya biyo baya a yau, babu sauran Sanatan jihar Kwara a APC, duk sun koma PDP sai dai shi Saraki din.
Discussion about this post