2019: Atiku ya kaddamar da takarar shugaban kasa

0

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya kaddamar da takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP.

Dubban magoya bayan sa sun cika filin wasa na Jimeta inda ya sha alwashin dawo da kassr nan a cikin hayyacin ta.

Atiku ya ce “za a fi tuna gwamnatin Buhari da asarar dubban rayuka fiye da wani amfani da gwamnatin ta samar.”

” A dalilin kashe-kashen da ka yi ta samu a kasar nan da ake ta danganta shi da ayyukan wasu ‘yan barandan makiyaya, mutanen da aka kashe a wannan mulki na APC sun fi wadanda aka kashe a kasashen Iraki da Afghanistan.” Atiku ya ce idan ya zama shugaban kasa zai kawo karshen irin wannan kashe-kashe.

Daga nan sai Atiku ya kara da nuna wani abin da ya kira babbar matsalar da gwamnatin Buhari ta haifar wato mummunan rabuwar kawuwan kabilun kasar nan, fiye da can baya.

Ya ce duk wadannan matsaloli ne da zai gaggauta kawar da su da zaran ya hau mulkin kasar nan.

Atiku zai fuskanci gwagwagwa da sauran ‘yan takara irin su Sule Lamido, Ahmed Makarfi da kuma irin su Rabi’u Kwankwaso da Aminu Tambuwal da ake tsimayen canja shekar su zuwa PDP kwanan nan.

Share.

game da Author