Farkon wannan makon ne Karamin Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, ya kaddamar da sabon jirgin sama da Gwamnatin Muhammadu Buhari ta ce za ta samar.
Jirgin mai suna Nigeria Air, ya samu kyakkayawar karbuwa daga magoya bayan gwamnatin, wadanda tuni suke ta cika kasar nan da murnar cewa Buhari ya yi rawar gani, musamman tunda Najeriya ta dade ba ta da kamfanin jirage na ta, tun bayan durkushewar Nigeria Airways.
Sai dai kuma wadansu dalilai masu yawa sun haifar da kakkausar sukar kafa sabon kamfanin, Nigeria Air.
Na farko dai Sirika ya tafi can Ingila ya kaddamar da jirgin, ba a nan Najeria ba. Na biyu kuma ya ce na ‘yann kasuwa ne, ba na Najeriya ba, domin kashi biyar bisa 100 kacal gwamnati za ta saka a matsayin hannun jarin ta a cikin kamfanin.
Sannan kuma, wata babbar mishkila ita ce, a halin yanzu babu jirgin ko daya, kuma ko masu hannayen jarin da za su zuba ma sai an nemo, har Dala milyan 300 Sirika ya ce ake bukata a zuba a matsayin jari.
Sannan maimakon a ga Sirika ya diro Najeriya da ko da jirgi kwaya guda ne, sai diro daga shi sai jakar sa, a jirgin haya, ba a Nigeria Air ba.
Wannan jirgi dai gwamnati ta ce sai ma 19 Ga Disamba sannan za a fara kawo guda biyar daga cikin su. Sannan a sake kawo saura a cikin shekaru uku.
A takaice dai kenan fasta hoton jirgi ce Minista Sirika ya kaddamar a Ingila ba jirgi ba. Dalili, sai nan da kusan watanni shida sannan a fara shigo da jiragen Najeriya.
Jama’a da dama na ganin cewa an yi azarbabin kaddamar da abin da babu, sai a mafarki ko a takarda kawai.
Wasu kuma na ganin cewa ai kawai farfaganda ce ake yi domin a shafa wa ‘yan Najeriya mai ga baki, gwamnatin APC ta na kamfe ne da batun jiragen kasa don neman zaben 2019.
Fitaccen mai zaben barkwanci Mike Asukwu, a cikin zane ya bayyana jirgin da cewa siyasa ce kawai aka yi wa ‘yan Nijeriya.
Haka da dama ba’arin masu sukar wannan gwamnati na ganin cewa mene ne abin yin azarbabin kafa abin da babu shi, kuma sai nan da watanni shida sannan a fara shigo da shi.
Tsohuwar Ministar Harkokin Ilmi a zamanain mulkin Obasanjo, Obey Ezekwesili, ta ce kafa kamfanin asara ce, kuma zurara makudan kudade ne a cikin rijiyar da ba mai iya kwasowa.
Obey ta ce kafa kamfanin ba zai amfana wa Najeriya komai ba, sai tafka asara kawai.
Ita ma jam’iyyar PDP ta yi fatali da shirinn kafa jiragen, wanda ta kira yaudara ce kawai da gwamnarin APC, saboda sun rasa abinda za su yi kamfen da shi domin a sake zaben su.
Haka kakakin PDP, Kola Obadiyan ya bayyana a jiya a cikin wata takarda da ya fitar.
Ya kara da cewa tusa ta kare wa budari, shi ya sa gwambatin APC ke kai gwauro tan a kai mari, wajen rinton ayyuka, bayan ko hadan ba ta da abin tinkaho da za ta nuna wa talakawa a shekaru sama da uku.
Ko ma dai me kenan, akwai kuskure a ce gwamnati ta daure gindin kafa wani kamfanin jirage, alhali Nigeria Airways na nan a durkushe ba ta tashe shi ba kamar yadda ta yi alkawari.
Ina makomar tsoffin ma’aikatan Najeriya Airways da aka yi wa alkawarinn biyan su hakkokin su na shekaru da ba a ba su ba?
Kada a ga laifin masu cewa gaba daya shirin duk farfagandar yakin neman zabe ce. Dalili, saurin me ake a kaddamar da abin da babu, guda daya ma ba a kawo an yi an gani a kasa ba, sai dai hoton tambari kawai.
Irin wannan sammakon ne Hausawa ke kira sammakon bukukuwa fa.
Discussion about this post