‘Yan adawa na amfani da rikicin makiyaya su na kulla min algungumanci -Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci daukacin shugabannin jam’iyyar APC zuwa gangamin yakin neman zabe na ranar karshe a zaben gwamnan jihar Ekiti da za a ranar Asabar mai zuwa.

Sun je ne domin su tallata dan takarar gwamna a karkashin APC, Kayode Fayemi.

Buhari ya roki ‘yan jihar da su kada kuri’ar su ga Fayemi, wanda ya ce yin hakan ne zai kawo musu yalwa da albarkar da za ta rika bibiyar jihar har shekaru aru-aru nan gaba.

Daga nan sai Buhari ya ce al’ummar Ekiti su yi kaffa-kaffa da masu kitsa karairayi da algungumanci a kan sa, su na yi masa sharrin cewa da gangan ya bari rikicin makiyaya da manoma ya yi kamari a kasar nan.

“Su na kulla min sharrin cewa wai ban yi komai a kan rikicin ba, saboda ni ma Bafulatani ne.”

“Amma wannan sharri ne kawai. Muna yin bakin kokarin mu domin ganin an samu sahihiyar hanyar magance wannan rikice-rikice.”

Buhari ya maida wannan raddi ne ganin yadda jam’iyyar PDP ta fito ta ce ya zuba ido ana kashe dimbin rayuka sakamakon rikice-rikicen makiyaya da manoma, ya ki yin komai.

Share.

game da Author