EKITI 2018: Sanatoci sun soki Buhari kan tura ‘yan sanda 30,000

0

Manyan masu rike da manyan mukaman shugabanci a Majalisar Dattawa, sun ragargaji Shugaba Muhammadu Buhari dangane da yadda ya bar Sufeto Janar ya tura dakarun ‘yan sanda har 30,000 a jihar Ekiti.

Mataimakin Shugaban Majalisa, Ike Ekweremadu da Mataimakin Shugaban masu rinjaye, Bala Ibn Na’Allah, duk sun nuna rashin cancantar tura wannan gayyar jami’an tsaro kamar za su je yakin duniya.

Sun yi mamakin yadda aka tura ‘yan sandan saboda zaben da za a yi rana daya, amma jihohin da ake kashe-kashe ba a maida hankali sosai a kan su, wajen tura musu jibgin jami’an tsaro ba, kamar Ekiti.

“Ta ya za a ce wuraren da ake kashe-kashe an tura musu ‘yan sanda kasa da 10,000, amma jihar da za a yi zabe ann tura ‘yan sanda 30,000 har da hada su da motocin yaki?” Inji Sanata Na’Allah.

Share.

game da Author