Mata a jihar Zamfara sun bayyana yadda rayuwarsu ta inganta sanadiyyar darussan da suka koya a shirin ‘Girls for Girls initiative (G4G)’ wanda asusun tallafawa yara kanana na majalisar dinkin duniya, gwamnatin tarayya da kungiyar UKAid suka shirya.
Wannan shiri na G4G an shirya ya shi ne domin wayar da kan mata da ‘yan mata a yankin arewacin Najeriya kan mahimmancin samun ilimin boko da yadda za su inganta kiwon lafiyar su.
Cikin jihohin da za su amfana da wannan shiri sun hada da Zamfara, Neja, Bauchi,Sokoto da Katsina.
Hadiza Isah dalibar makarantar firamaren Tudun Wada Model Primary School, dake Tsakuwa a karamar hukumar Talatan Marafa ta bayyana cewa shirin G4G ya koya mata yadda zata tsaftace jikin ta musamman a lokacin da take haila.
Ta ce sun koyi yadda ake amfani da auduga yayin da suka haila, yadda ake dinkata da yadda za su iya adanashi domin su yi amfani da shi domin wani watan.
Aina’u Attahiru mai shekaru 11 kuma dalibar makarantar firamaren Nizzaniya a jihar ta bayyana cewa darussan da ta koya a shirin G4G sun hada da wanka, wanke hakora, wanke hannu kafin a ci abinci da bayan an ci abinci sannan da bayan an yi amfani da ban daki.
Ita kuwa Fatima Mohammed mai shekaru 14 ta ce a dalilin wannan shiri ta koyi sana’ar hannu sannan tana so ta koma karatun Boko.
Ta ce ta koyi yadda ake hada Sarkar wuya,sabulun wanke-wanke da man shafawa wanda takan siyar kuma ta sami kudin da mahaifanta ke amfani da su wurin kula da gida.
A karshe jami’in shirin Tayo Fatinikun yace a dalilin wannan shiri da suka fara a watan Agustan 2017 sun sami nasarar wayar da kan ‘yan mata 4,399 a makarantun jihar sannan shirin ya sa ‘yan mata 165 makaranta.