Muddun aka yi murdiya a zaben Ekiti, zaben 2019 ma zai zama kila-wa- kala – PDP

0

Shugaban jam’iyyar PDP, Uche Secoundus ya gargadi hukumar zabe ta Kasa da jam’iyya mai mulki, APC cewa kada su kuskura su murde zaben jihar Ekiti dake tafe cewa muddun aka yi haka to ko a sallama wa zaben 2019 kawai domin wai ba za ayi shi ba.

Secondus ya bayyana haka ne da yake kaddamar da kwamitin da za ta kula da shirye-shirye da sa ido a zaben.

mambobin kwamitin sun hada da gwamnan Gombe, Ibrahim Dankwambo, Ahmed Makarfi, Atiku Abubakar, Ibrahim Shekarau, David Mark, Sule Lamido da dai sauran su.

” Muna sane da shirin da APC ke yi na murde zaben. To ko su sani cewa Ekiti ta fi karfin su. Idan ko suka kikace kan niyyar su to ko zaben 2019 ma zai zama kila-wa- kala.”

Za ayi zaben gwamna a jihar Ekiti ranar 14 ga watan Yuli.

Share.

game da Author