Ministan Harkokin Mata, Aisha Alhassan ta bayyana wa gungun ‘yan jam’iyyyar APC a jihar Taraba cewa ko tantama bata da shi jam’iyyar APC ce za ta ci gaba da mulkin Najeriya har illa ma sha Allah.
Bayan haka kuma ministar ta shaida musu cewa zata sake fitowa takarar gwamnan jihar Taraba a 2019.
” Dama ko a 2015 nine na lashe zaben gwamnan jihar, Allah ne bai yi zan zama gwamna ba. Amma kuma akwai wata damar kuma gashi ta zo yanzo. Zan sake takara a 2019.
” Zan bi mazabu na sau da kafa, in tabbatar duk abin da ake bukata ya samu kafin wannan lokaci daga nan kuma sai mu tunkari zaben 2019 gada-gadan. Dama kuma zaben shugabannin jam’iyya ne ke gaban mu yanzu.
” Da zarar mun kammala zaben sai mu karkata kuma zuwa zaben gamagari.
Idan ba a manta ba minista Aisha ta taba fadi cewa ba ta da gwani a siyasar Najeriya kamar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.