Masu garkuwa sun saki mata da ya’yan Kwamishinan Zamfara

0

A yau Litinin ne rundunar ‘yan sanda jihar Zamfara ta sanar da sakin mata da ‘ya’yan Kwamishinan matasa da wasanni na jihar Zamfara, Abdullahi Gurbin Baure a gidan sa dake Baure.

Idan ba a manta ba wasu ‘yan baranda sun farwa gidan kwamishinan matasa da wasanni na jihar Zamfara, Abdullahi Gurbin Bore a kauyen Gurbin Bore dake jihar in da suka yi garkuwa da matarsa da ya’yan sa 6.

Kwamishina Abdullahi ne ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin labari da wannan abin takaici inda ya bayyana cewa, maharan sun far wa gidan sa ne da karfe 1:30 na daren Talata.

Ya ce an sace matan sa daya, ‘ya’yan sa uku da wasu yan’uwan sa uku da ke zama da iyalan sa, sannan har yanzu masu garkuwan ba su tuntube shi ba.

‘Yan sandan sun ce ba a bada ko sisi ba wai don fansar wadannan bayin Allah da masu garkuwan suka sace.

Share.

game da Author