Tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar ya sanar da nada tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daniel darektan Kamfen din sa.
Atiku ya bayyana cewa ya nada Daniel ne ganin cewa ya na da farin jini da dattaku sannan kuma ga kima a musamman tsakanin mutanen yankin kabilar ‘yarbawa.
Atiku ya ce yayi haka ne domin ya maida hankali wajen yin wasu abubuwan da ya shafi abin da ya sa a gaba inda shi Gbenga zai taimaka masa wajen harkokin siyasa da kamfen din sa.
Discussion about this post