WAIWAYEN NASARORIN 2015
Lokacin da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta cika shekara daya kan mulki, watan Mayu, 2016, Fadar Shugaban Kasa ta bayyana nasarori 75 da shugaban Muhammadu Buhari ya cimma a adadin watanni 12 da ya yi a karagar mulkin kasar nan. A matsayin murnar bikin zagayowar cikar shekara guda da kama aiki wanda kuma Hakan ya yi daidai da murnar bikin ranar Dimokradiyya na 2016. Jadawalin nasararorin da ya cimma kamar yadda aka wallafa a shafin Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN), sun hada kamar haka:
TSARO:
Mayar da cibiyar rundunar tsaro ta sojin kasa zuwa Maiduguri, tun a watan Mayun 2015 ya agaza wajen samun nasarar murkushe masu tayar da kayar baya a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan.
A Fabarairun 2016, adadin mutanen da rundunar sojin kasar nan suka ceto daga hannun masu tayar da kayar baya sun kai kimanin 11,595
Tun Disambar, 2015, dakarun sojin Nijeriya suka samu galabar kwato duk wani yanki da kungiyar Boko Haram suka kwata.
Namijin kokarin samun hadin kan kasashen da ke makotaka da Nijeriya domin yakar Boko Haram da kuma masu tayar da kayar baya mai dauke da dakarun sojin hadin gwiwa 8,500 a N’Djamena babban birnin kasar Chadi da Nijeriya ke jagoranta.
Nijeria ta samar da tsabar kudi har dalar Amurka Miliyan 21 ga sojojin hadin gwiwar tun a watan Yunin 2016 kana kuma daga bisani aka kara musu adadin Dalar Amurka Miliyan 79, wanda idan aka hada ya zama jimullar dalar Amurka Miliyan 100.
Samun goyon bayan kasashen ketare domin yaki da ta’addanci gami da samun tallafi ga wadanda abin ya shafa da kuma yankunan da abin ya faru, sakamakon ganawar da shugaban Buhari ya yi shugabannin kasashen G7 da kuma wasu masu karfin fada a ji.
A Mayun 2016, Nijeriya ta shirya taron shiyyoyi akan tsaro domin inganta harkar jami’an soji na yakI da Boko Haram tare da neman dauki daga kasahen ketare don yin garambawul ga sansanin ‘yan gudun hijira da kuma sake gina yankin Arewa maso Gabas.
A Yunin 2015, kasar Amurka ta ayyana bayar da tallafin dala miliyan 5 domin yakI da kungiyar Boko Haram.
A Afirilun 2016, yayin kai zigaya ga Ms Samantha Power, Ambasadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya na Nijeriya, Kamaru da Chadi ya ayyana cewa gwamnatin Amurka ta kara bayar da tallafin dala Miliyan 40 a matsayin dauki ga yankin da rikicin Boko Haram ya shafa.
Ana tsaka da tantance daukar ‘yan sanda 10,000 wanda Hakan zai cike gibin da aka samu a rundunar ‘yan sanda ta kasa.
Kyautata tare da inganta rundunar sojin kasa wanda hakan ne sirrin samun nasarar karya kashin bayan Boko Haram.
Dawo da martabar dakarun sojin kasar nan wanda Hakan ya sa kasar Amurka da Birtaniya suka lafta makudan kudade domin yakI da ta’addanci tare da bayar da goyon baya wanda a baya suka janye ga gwamnatin baya. Hatta gwamnatin kasar Isra’ila ta nuna sha’awar bayar da goyon baya domin yakar ta’addanci.
Samar da baburan yaki ga rundunar soji wanda zai ba su damar shiga yankuna mai nisa da mota ba za ta iya kai wa ba.
Tattaki takanas zuwa wasu kasashe tare da kyautata alaka da kuma dankon zumunci wanda Hakan ya Hakan ya sa aka samu gagagrumar nasarar yarjejeniyar yakI da ta’addanci a Nijeriya.
An janye shingen tsaro da kuma dokar ta-baci wadda suka hana mutane ‘yancin walwala.
Bibiyar harkokin yankin da ake fama da matsalar tsaro ta hanyar amfani da na’urar tauraron dan adam domin taimakawa wajen yakar ta’addanci da kuma makiya.
Ziyartar kasashen da ke makotaka da Nijeriya ya nuna namijin kokarin shugaban kasa na karya kashin bayan kungiyar Boko Haram wanda ya hada da yanke kafar samar musu da abinci. Wanda kuma hakan ya samu ne da taimakon rundunar hadin gwiwar tsaro ta kasa da kasa.
Wani gagarumar nasarar da aka samu shine goyon bayan wasu kasashe da shugaban kasa ya samu na yakI da hada-hadar kananan bindigogi da kuma sauran kananan makamai.
Da taimakon kasar Amurka rundunar sojin Nijeriya sun samu kyautar motocin sulke na yakI guda 24 da suka rika ba su kariya daga ta’annatin bama-bamai da ake dasawa. Wanda a halin yanzu an samu karancin rasa ran jami’an soji.
Sakamakon ganawa da kasashe masu karfin tattalin arziki na G7 an cimma nasarori kamar haka; musayar bayanan tsaro na sirri, sabbin dabarun tsaro ga sojoji, hada-hadar makamar da kuma samun kyautar makamai. Tare da sake sabunta wani kudiri na gwamnatin da ta gabata wanda ake ba wa tsageru damar kare albarkatun kasa maimakon dakarun sojin ruwa.
Shugaba Buhari ya gabatar da wani daftari da ya lamincewa jami’an soji hada kai da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar ga dukiyar kasa wanda tuni an fara girbar ribar wannan kudiri.
An kama gawurtattun tsagerun da ke tarwatsa bututun mai a jihar Legas kwanan nan da taimakon hadakar jami’an tsaro da sojoji suka jagoranta.
Gwamnati ta sabunta yaki da ta ke yi da masu satar danyen man fetur.
Dakarun sojin ruwa sun yi gagarumar nasarar gano wani bututu da masu satar danyen mai suke amfani da shi. Wannan farmaki ya agaza wajen gudanar magudanar ruwan Nijeriya da kuma habaka kudin haraji ga gwamnati.
Samar da nagartattun makamai na zamani domin magance fasa bututun mai tare da samar da jami’an sintiri domin magance matsalar.
Kawo karshen balahirar masu rajin kafa kasar Biafra.
Inganta harkar tsaron jami’an ‘yan sanda. A halin yanzu muna da rumbun kwasar bayanai da kuma kuma bin diddigin salula.
Zaburar da jami’an shige da fice domin dakatar da laifukan iyaka da iyaka.
Jami’an sintiri na NSCDC sun kara matukar kwazo ta hanyar hana fasa bututun mai gami da kama masu satar mai da dama.
Kafa rundunar hadin gwiwa na tsaro da suka hada da hukumomi da dama domin magance matsalar tsagerun makiyaya.
Sa ido tare da daukar muhimman matakai domin kaucewa rikicin kabilanci a Nijeriya.
RASHAWA
Nasarar lashe zaben shugabancin kasa da ya yi a kakar zaben 2015, a matsayinsa na tsayayye kuma jajirtaccen shugaban da ba ya karbar wargi ya jefa tsoro a zukatan barayin gwamnati da suka rika dawo da dukiyar da suka sata a gwamnatocin baya.
Domin kawo karshen cin hanci da rashawa shugaban Buhari ya kafa kwamitin masu ba shi shawara akan yaki da cin hanci da rashawa.
Yaki da cin hanci da rashawa na samun nasarar domin gabatar da manyan kusoshin gwamnati a gaban kotu. Kana kuma gwamnati na yin taka-tsantsan wajen bin doka da oda akan wannan yaki da rashawa.
Shugaba Buhari ya nemi goyon bayan hukumomi da dama kamar bankin duniya da hukumar lamuni ta duniya, hukumomin tsaro, kasashen yammaci da kuma wasu kasashen da muke da kyakkyawar alaka da su agaza wajen dawo da dukiyar kasa da aka sata aka kai can aka jibge.
A taron birnin Landan da aka gabatar akan yaki da cin hanci da rashawa shugaban Buhari ya ayyana cewa kasar Nijeriya za ta fara gabatar da cikakku kuma yardaddun tsarin musayar bayanai.
A farkon shekarar 2016, shugab Buhari ya ziyarci Gabas ta Tsakiya domin neman su dawo da dukiyar kasa da aka sata aka kai can, kana kuma su dawo da barayin gida Nijeriya domin fuskantar matakin shari’a. A watan Janairu, Nijeriya da Hadaddiyar Daular Larabawa sun rattaba hannu akan yarjejeniyar dawo da mai laifi ga kasar sa, musayar fursunoni da kuma goyon baya akan hukunta masu laifi.
A Maris 2016, Gwamnatin Tarayya da kuma Gwamnatin kasar Suwizalan sun rattaba hannu akan dokar dawo da dukiyar sata da aka sata daga nan aka kai can. A karkashin wannan yarjejeniya aka kasar Suwizalan za ta dawo da tsabar kudi dalar Amurka Mmiliyan 321 da iyalan tsohon shugaban kasa Marigayi Sani Abacha suka mallaka.
A watan Maris na 2016, shugaban kasa ya kafa kwamitin binciken kwangilolin da ofishin mai ba wa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro ya bayar daga 2011 zuwa 2015 an dawo da sama da Naira biliyan 7 daga kamfanoni da kuma al’umma.
TATTALIN ARZIKI
Bijiro da tsarin asusun gwamnati daya tilo ya samar da gagarumar nasarar gano harajin da gwamnati ke samu da kuma shige da ficen kudade. Tsakanin Watan Yunin 2015 zuwa Afirilun 2016 wannan tsari ya haifar da Naira Tiriliyan 3 a asusun gwamnatin tarayya.
Domin gyatta haramben kudade shugaban kasa ya ya umarci rufe asusun ma’aikatu gwamnati da dama da kuma hukumomi domin kawo karshen zurarewar kudade da kuma cin bulus.
Sabon tsarin bin diddigin kudaden matatun man Nijeriya da a baya suke da asusu sama da 40 ya sa yanzu matatun mai na yin lissafin keke-da-keke ta hanyar wallafa bayanin kudaden da suka samu na wata-wata.
Shugaban kasa ya tsohe kafar haramtattun hada-hadar mai ba bisa ka’ida ba, wanda wasu tsirarun attajirai ke azurta kansu da biliyoyin daloli.
Domin kai dauki ga halin ni -‘ya-sun da ‘yan Nijeriya ke ciki shugaban kasa ya umarci babban bankin CBN a watan Satumba da ya fitar da Naira 689.5 a matsayin tallafi ga jihohi 27 domin su biya albashi.
Domin daidaita tattalin arziki da kuma rage talauci a watan Afirilun 2016 shugaba Buhari ya amince da kara bayar da tallafin gaggawa a yayin da jihohi suke tsaka da fama da halin kaka-ni-ka-yi.
Adadin ma’aikatan bogi sama da 34,000 aka kora daga ma’aikatun gwamnatin tarayya wadanda suke daukar kusan Naira Biliyan 2.29 a kowane wata.
A 2015, shugaban Buhari ya hana daukar nauyin jami’an gwamnati domin zuwa aikin Hajji, wanda wannan mataki ya janyo gwamnati na samun rarar Dalar Amurka miliyan 30.
Ta hanyar yin amfani da sabuwar lambar asusun Banki ta BVN ya sa an samu nasarar korar ma’aikatan bogi kana kuma aka gano ma’aikatan gwamnati da ke satar dukiyar gwamnati.
An tsara yadda tallafi zai rika zuwa ga talaka ta hanyar samun bayanai daga hukumar tsara tattalin arzikin kasa na mataimakin shugaban kasa da kuma Bankin Duniya.
Grambawul tare da sabunta matatun mai zuwa sabuwar alkibla suka dawo hayyacinsu na ci gaba da tacewa gami da hankada Gas da fetur da sauran ma’adinai.
Rage yawaitar arasa mara dalili a hukumar NNPC da kaso 50 kamar yadda aka gani a watan Maris 2016
Samar da bayanin kididdigar kudin hukumar NNPC daga 2011 zuwa 2014 domin samun bayanin keke-da-keke.
Samar da wakilai masu bin diddigin yadda gwamnatin tarayya ke kashe kudade domin kauce wa rashawa.
Sake sabunta hukumomin kula da kwangiloli domin kaucewa sanya son zuciya da aringizon kudade.
Soke yadda ake hada-hadar albarkatun man fetur zuwa kasashen ketare ta hanyar bullo da sabon tsari da kai-tsaye gwamnati za ta saya ko ta sayar daga hannun wata gwamnatin ba tare da wakilai ba, wanda Hakan ya sa gwamnati ke samun rarar dalar Amurka Biliyan 1.
Saita alkiblar matatun mai na Warri, Fatakwal da kuma Kaduna wanda a halin yanzu suke tace litar mai miliyan 7 kowacce rana.
Gyara bututun hankado mai da suka yi shekaru 6 ba sa aiki.
Gyara bututun mai na Escravos/ Warri da Bonny/Port Harcourt
Samar da tsarin daidaita farashin man fetur domin cimma muradun kasuwa.
Gyatta tsarin rarraba man fetur da kuma cire tallafin mai
Fadada matatun mai da kuma adana shi saboda fargabar yankewar sa a nan gaba.
Samar da tsarin dillancin gas ta yadda za a amfana da muhimman ayyuka da kuma hanzarta amfana da shi ta fuskar makamashi.
LANTARKI
A karkashin gwamnatin Buhari gwamnatin tarayya ta amince da ranto Yuro miliyan 50 daga gwamnatin Faransa domin maganta matsalar tabarbarewar lantarki a Nijeriya.
Nijeriya ta sanya hannu a kan yarjejeniyar dala miliyan da bankin duniya domin inganta lantarki.
Ma’aikatar samar da lantarki daga hasken rana ta kasar Chana ta yi yarjejeniya da gwamnati domin kafa cibiyar kasuwancin samar da lantarki a Nijeriya.
Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu da gwamnatin kasar Chana domin samar da lantarki a Nijeriya.
MUHALLI
Shugaba Buhari ya rattaba hannu da Majalisar Dinkin Duniya domin wanke dagwalon yankin Ogoni saboda gurbata muhalli da albarkatun mai ke yi.
Ci gaba da assasa shuke-shuke domin kaucewa afkuwar sahara a yankunan Arewa.
SHARI’A.
Tun da shugaban kasa ya kama aiki Buhari ya ke jaddada matsayin sa na bin doka da oda da kuma raba mukamai bisa la’akari da bambance-bambancen al’umma.
MUKAMAI
Shugaban kasa ya karkata ga raba mukaman gwamnati bisa cancanta.
Nada sabbin alkalai a manyan kotunan Tarayya.
MARTABAR KASA
Ya na shiga ofis shugaban Buhari ya fara tafiye-tafiye zuwa kasashen Afirka da Turai domin sake gyara alakar Nijeriya da sauran kasashe.
Shugaba Buhari ya ci gaba da kokarin farfado da martabar Nnijeriya a idanun kasashen duniya ta hanyar buga misali da zaben 2015 da aka gudanar cikin lumana da kwanciyar hankali.
Shugaban kasa Buhari ya goyi bayan kawo dan Nijeriya Dakta Akinwumi Adesina, a matsayin shugaban Cigaban Bankin Afirka.
2017 A TAKAICE:
Bayan cikar gwamnatin Buhari shekara biyu kan mulki, an yi wani kasaitaccen biki a Fadar Shugaban Kasa, inda aka kaddamar da wani littafi da Ministan Sadarwa, Bolaji Abdullahi ya rubuta.
Littafinn dai na kunshe da wasu nasarorin Shugaba Muhammadu Buhari da kuma labarin yadda Jonathan ya ci nasarar zama shugaban kasa da kuma yadda ya yi sakacin da ya kai shi ga faduwa zabe.
Bayan kammala taron kaddamar da littafin ne sai Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, ya bayyyana cewa har yau nasarorin wannan gwamnati mai mulki ba su ko kama kafar nasasrorin gwamnatin sa ba.
Jonathan ya bayyana haka ne ta bakin Kakakin Yada Labaran sa, Ikechukwu Eze, ya na mai cewa sukar da gwamnan jihar Borno ya yi wa gwamnatin sa cewa ba tagari ba ce, ba komai ba ne sai ‘‘hauragiya da rashin kaifin tunani.”
Tsohon shugaban kasar ya yi wannan martani ne ga jawabin da gwamnan Barno, Kashim Shettima ya yi a wurin kaddamar da littafin da Bolaji Abdullahi, kakakin yada labaran jam’iyyar APC, ya rubuta, wanda aka kaddamar a Abuja.
Jonathan ya ce lokaci ya yi da gwamnan Barno zai fito flli ya fada wa duniya rawar da ya taka wajen sace ‘yan matan Chibok.
“Sai Kashim Shettima ya fito yanzu ya fada mana idan Jonathan ne ya sa shi tura daliban Chibok makaranta su yi jarabawa, alhali gwamnatin tarayya ta bada dokar cewa kada jihohin nan uku, Barno, Yobe da Adamawa su sake su kai dalibai su zauna jarabawar WAEC a yankunan da babu tsaro.”
Littafin dai ya na kunshe ne da labarin yadda Jonathan ya ci nasara zama shugaban kasa da kuma yadda ya yi sakacin da ya kai shi ga faduwa zabe.
Jonathan ya bayyana littafin da cewa kundin soki-burutsu ne kawai.
2017: SHEKARAR KASHE-KASHE DA GARKUWA DA JAMA’A
A wannan shekara kusan abin da ya fi daukar hankalin jama’a a Najeriya shi ne abubuwa uku ko hudu. Na farko akwai kashe-kashe a yankin Arewa ta Tsakiya, kamar a Taraba, Benuwai , Adamawa da kuma Nasarawa.
Idan aka mirgina Arewa kuwa, jihohin Kaduna da Zamfara sun kasance cikin tashin hankalin kashe-kashen mahara, inda abin maimakon a samu sassauci, sai kara munana ya ke yi a cikin 2018 ne kuma har yanzu.
Kwanan nan Sanata Shehu Sani daga jihar Kaduna ya bayyana cewa abin da ke faruwa a Arewacin Najeriya ba shi da bambanci da abin da ke faruwa a kasar Syria, wajen karkashe mutane ana korar su daga muhalin su.
A shekarar 2017 an dakushe kaifin kungiyar ‘yan taratsin IPOB, masu so a raba Najeriya su maida na su kason Jamhuriyar Biafra.
An samu gudanar da ayyuka a kasar nan, sai dai kuma akasari duk a yankin Kudu-maso-yamma, musamman a Lagos ne aka fi gudanar da bimbin ayyukan.
Matsalar sace matafiya a yi garkuwa da su ta kara munana a 2017. Har ta kai a na bi gidaje da kananan garuruwa ana sace mtane da rana tsaka ba sai cikin dare ba.
2018: SHEKARAR HISABIN BUHARI
An shiga 2018 dauke da niki-nikin matsalolin kasar nan da ba a kai ga warwarewa batun daga 2015 har 2018. Da yawan matsalolin sun kara zafafa, wasu kuma sun kara muni.
Boko Haram sun kara zafafa hare-hare, a daidai lokacinn da ake cewa an ga bayan su. Sun shiga har cikin makarantar sakandare ta Dapchi, a jihar Yobe sun sace Dalibai 206. Kuma har yanzu duk da cewa an cimma yarjejeniya sun maida daliban, Boko Haram ba su daina kai harin katilan-makatulan ba.
Kashe-kashen a Arewa ta Tsakiya zuwa jihar Kaduna da kuma Zamfara sunn ci gaba da kara muni, duk kuwa da sojoji da aka jibge a jihohin.
CIKAS DIN GWAMNATIN BUHARI:
Kisan mabiya Sheik Ibrahim El-Zakzaky cikin Disamba, 2015. An kashe daruruwan mabiyan sa, ciki har da ‘ya’yan sa hudu. An lahanta shi da matar sa Zeenat kuma ana ci gaba da tsare su.
Hakan ya sa mabiyan sa yi wa Abuja shiga-farin-dango suna zanga-zanga a kowace rana, banda Asabar da Lahadi. Akwai alamomin cewa wannan zanga-zanga da wuya a kawo karshenta cikin girma da arziki.
Dalili kuwa shi ne, tun daga Disamba, 2016 kotu ta sha bai wa gwamnatin tarayya umarnin a saki malamin tare da matar sa su fita su nemi magani. Amma gwamnati ta yi kunnen-uwar-shegu da umarninn kotu, sai ma maka shi kotu da aka yi kwanan nan.
A daya gefen kuma mabiyan sa sun ce ko za ta dagule ba za su fice daga Abuja ba, sai idan an saki jagoran na su. Ya zuwa yau sun shiga kwana 140 kenan su na zanga-zanga, duk kuwa da cewa an samu asarar rayuka ciki har da wakilin El-Zakzaky na Sokoto, Malam Kasimu, hakan sai ma karfafa wa mabiyan na sa kara shigowa Abuja aka yi.
KASA MAGANCE KASHE-KASHE
Matsalar kashe-kashe a yankinn Arewa, musamman a Kaduna da Zamfara ta yi muni fiye da zamaninn Goodluck Jonathan. Akwai hare-haren makasa da ke boye cikin dazukan Zamfara da kuma Birnin Gwari. Sannan kuma an samu fantsamar masu garkuwa da jama’a sosai a zamanin Buhari, musamman a tsakanin Abuja da Kaduna, Neja da da sauran garuruwa.
YAJIN AIKIN LIKITOCI DA MALAMAN ASIBITI
Har yau wannan matsala ta ki ci ta ki cinyewa, gwamnati ta kasa tsayawa a fuskanci matsala a lokaci guda domin a warware ta. Duk wasu alkawurra da Buhari ko jam’iyyar APC ta yi dangane da kiwon lafiya, sun zama bulkara.
Akwai alkawarin rika kashe naira dubun hamsin kan kowane dan Najeriya a fannin lafiya a kowace shekara. Shekara uku kenan babu wata alamar da ke nuna hakan ya tabbata.
Masu hannu da shuni da manyan ma’aikatan gwamnati da ‘yan siyasa sai ficewa waje suke yi ganin likita. An bar masu karamin karfi cikin zulumin nema wa kan sa mafita idan rashin lafiya ta riske shi.
KAKA-GIDAN SOJOJI A FADIN KASAR NAN:
Kusan jihohin da ba a girke sojoji su na gaganiyar aikin tsaro ba, ba su wuce shida ba a fadin kasar nan, idan ma sun kai din. Wannan kuwa babban cikas ne ga gwamnatin dimokradiyya.
Matsalar tsaro har yanzu ta yi wa mulkin Buhari tarnaki da dabaibayi, kamar yadda ta yi wa mulkin Goodluck Jonathan.
A fili ta ke cewa ‘yan danda sun kasa wanzar da tsaro a cikin al’umma wanda hakan ya sa tilas an tattago sojoji daga cikin barikokin su ana girke su da kafa musu sansanoni a cikin fararen hula domin kokarin kakkabe maharan sari-ka-noke da ‘yan samame da kuma kashe-kashen kabilanci da na siyasa.
Kafa sojojin da ake ci gaba da yi a fadin kasar nan, har yau bai nuna alamar kawo karshen kashe-kashe ba.
ZARGIN CIN ZARAFIN MATA A SANSANIN GUDUN HIJIRA
Rahoton da Kungiyar Kare Hakkin Jama’a ta Amnesty International ta fitar cikin makon da ya gabata, ta zargi sojojin Najeriya da cin zarafin mata masu gudun hijira da ke zaune a sansani daban-daban na kasar nan.
Gwamnatin Najeriya ta fito ta karyata, yayin da ita kuma kungiyar ta tattara wasu daga cikin wadanda aka ci wa zarafin ta kai su Abuja suka bayyana wa manema labarai irin halin da ake ciki, ko kuma aka shiga a hannun sojoji a sansanonin masu gudun hijira.
KASA HUKUNTA WADANDA AKE GURFANARWA
Shekaru uku kenan ana kama wadanda ake zargi da wawurar kudade a zamanin gwamnatin Goodluck Jonathan, ana kwace kudade ko kadarori, amma har yau ko daya daga cikin jiga-jigan gwamnatin da ta gabata ba a daure ba.
Ga kudi da kadarori an kama a hannun wanda ake zargi, amma matsalar rashin kwakkwaran shiri na yi musu hukunci a kotu ya sa an kasa hukunta kowa.
Kwanan nan Buhari ya ce zai kafa wasu kotuna na musamman, tsarin da tuni masu dogon tunani suka tabbatar da cewa ba zai yiwu ba, domin irin yadda ya ce zai yi, ba tsari ba ne na dimokradiyya, kuma Majalisa ba za ta amince a yi haka din ba.
RABUWAR KAWUNA A JAM’IYYAR APC
Zaben shugabannin jam’iyyar APC da aka gudanar kwanan baya, ya fito da babbar barakar da ke cikin jiga-jigan jam’iyyar da kuma su kan su sauran mambobi.
An yi zargin rashin adalci a fili, kuma irin yadda aka gudanar da zaben ya yi munin da ya raba kawunan ‘yan takara, shugabanni da kuma masu rike da gwamnati a cikin su.
Ko ranar Asabar da ta gabata sai da ‘yan Sabuwar PDP da suka taimaka wa APC ta kafa mulki, suka gudanar da taron nema wa kan su mafita daga cikin rashin adalcin da suke ganin gwamnatin Buhari na yi musu.
Kuru-kuru kuma talakawa sun nuna cewa a wannan karo a zaben 2018 ba za su bi umarnin Buhari su yi ‘sak’ ba. Cewa su ke yi duk inda nagari ya ke, ko ma wace jam’iyya ce, shi za su zaba.
MATSALAR DALIBAN DA KE NEMAN SHIGA JAMI’A
Gwamnatin Goodluck Jonathan ta yi rawar-gani wajen kafa Jami’o’in Gwamnatin Tarayya har 13 a fadin kasar nan. Akasarin gwamnonin PDP na lokacin kuma sun kafa jami’o’i na jihohi. Domin tun a lokacin sun fahimci hakan ne kawai zai bai wa matasa damar shiga jami’a bayanb sun kammala sakandare.
A karkashin gwamnatin PDP an samu jami’o’i biyu a Katsina, biyu a Kano, biyu a Jigawa, daya a Gombe da sauran jihohi da dama.
Zuwan gwamnatin Buhari an kara samun yawaitar dalibai masu neman shiga jami’a. sai dai kuma a cikin watan Janairu, 2019, Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa daga cikin dalibai milyan 1.6 da suka rubuta jarabar JAMB ta shekarar 2018, kashi 35 bisa ne kadai bisa 100 gwamnati za ta iya dauka zuwa jami’o’i. Wannan kuwa ba karamar matsala zai haddasa ba.
Sannan kuma hakan ya nuna akwai bukatar ko dai a kara yawann adadin wadanda za a dauka, ko kuma gwamnatin APC ta fadada jami’o’in ko a kara gina wasu a jihohin da ba a kafa ba. Ko kuma a yi duka ukun.
MATSALAR TSADAR RAYUWA
Masu karamin karfi na ci gaba da kokawa cewa har yau ba su ga wani canji ba, sai ma kara shiga halin kunci da suka yi. Da dama na ganin cewa wannan gwamnatin masu kudi ne kawai ke cin moriyar ta. Domin duk ta inda aka tsauwala wa kaya kudi, to talaka kadai abin zai shafa.
Kudin fetur da kananzir da kayan abinci da na masarufi duk ya tashi bayan hawan Buhura kan mulki. Dala ta kai naira 360 kuma babu ranar sassauci. Duk abin da mai kudi ke so zai iya fita kasar waje ya yi.
A cikin gida talakawa na jin haushin yadda aka kasa daure wanda aka kama ya saci bilyoyin nairori, amma a bangaren talakawa kwanstam sun a harbe duk wanda aka gani a guje dauke da dakon shinkafa ko da buhu biyar ne daga kan iyakar kasar nan. “Shin doka a kan talaka kadai ta ke ne?” Inji wasu da dama.
KALLON DA AREWA KE WA GWAMNATIN BUHARI
Ana kukan cewa jihohin da suka dirka wa Buhari har ya samu ya ci zabe, har yau ba su ga wani gagarimin abin a zo a gani daga gwamnatin APC ba. Jihohi kamar Kano, Katsina, Sokoto, Jigawa, Kaduna, Bauchi da sauran wasu da dama ana samun yawaitar korafin cewa Gwamnatin Buhari ta maida Jihar Legas kadai ‘yar lelen ta.
Yawancin jihohin Arewa idan ka shiga ka ce a nuna maka wani abin da za a yi tinkaho da shi gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi musu a cikin shekaru uku, har cikin aljihu sai an laluba ana nema amma a rasa.
Da dama na ganin sakacin Buhari, ganin yadda mataimakin sa ke samun dama, a duk lokacin da Buhari ba ya kasar nan, sau uku mataimakin sa Yemi Osinbajo na sa hannun amincewa a kafci makudan kudade a narka wajen gudanar da manyan-ayyukan da kakaf a Arewacin kasar nan ba a kashe kwatankwacin su a shekara uku ba.
KUKA DA OSINBAJO
Har ila yau, duk da haba-haba da mataimakin shugaba Buhari, Yemi Osinbajo ke yi da jama’a a duk inda ya shiga, ‘yan Arewa na zargin sa da nuna bangaranci.
A fili ta ke cewa duk ‘yan Arewa da Buhari ya nada a kan mukamai, Osinbajo ne ke daure gindin cire su, kuma sai ya bari Buhari ba ya kasar hakan ke faruwa.
An cire Shugaban Hukumar Inshorar Lafiyar Ma’aikatan Gwamnati, wanda dan jihar Buhari ne kuma ya ke a karkashin Ministan Lafiya dan yankin Osinbajo.
Bayan Buhari yac dawo, an yi ta kai ruwa rana kafin daga bisani aka maida shi.
Bayan shi kuma an cire Shugaban Hukumar Kula Da Hannayen Jarin Kamfanoni, wanda shi ma a nan, rigima ce tsakanin sa da Ministar Kudade, Kemi Adeosun, ‘yar yankin Osinbajo. An cire shi a lokacin da Buhari ba ya kasar, kuma shi ya nada shi.
AIKIN-BABAN-GIWA
Da yawan mutanen da aka yi hira da su a waya da kuma gaba da gaba, sun nuna haushi jin cewa gwamnatin Buhari ta sha alwashin farfado da kamfanin jiragen sama na Nigerian Airways.
“Yanzu saboda Allah da kamfanin jiragen sama da gaggauta gyara titin Kano zuwa Gwarzo zuwa Malumfashi wane ya fi muhimmanci ga talakan Kano, Katsina, Sokoto da Zamfara da Kebbi?
“Talaka za a gyara wa jiragen sama ko attajirai? Shin wai me ya sa mutumin nan ba zai gaggauta inganta mu ba, sai masu hali ya fi damuwa da su? Shikenan sai dai mu zabe su, daga baya su rika hawan jirage su na bar mata titi a farfashe kenan?” Inji Sani Muhammad, wani tsohon direban da ya dade ya na jigila daga Kano zuwa Sokoto.
Shi kuwa Malam Aliyu Sani, dan kamasho ne a Kano, cewa ya yi, “yanzu don Allah ba abin kunya ba ne a ce gwamnatin da talakawa ke tinkaho da ita, amma ta kasa gyada ko da tashar mota daya a fadin Arewa, sai ta koma gyaran jirgin sama.
“Babu wanda ya kai mu zafin biyan haraji, amma ko Abuja ka je, za ka ga tashar mota ba ta da bambanci da matattarar ‘yan sholisho, saboda kawai kuri’inmu ake so, ba sonnkyautata mana ba.
ALAMOMIN RAGUWAR FARIN JININ BUHARI
Yayin da magoya bayan sa ke ganin cewa har yanzu Buhari na nan da dimbin magoya bayan sa. Da daman a kuma ganin cewa farin jinin san a raguwa sosai musamman a soshiyal midiya da kuma irin yadda talakawa ke korafin matsin lambar matsalar tattalin arzikin da su ke fama da ita tun bayan hawan Buhari kan mulki.
Irin yadda aka rika yi wa wasu na jikin sa bore a zaben shugabannin jam’iyya ya nuna hakan.

Sannan kuma a baya musamman a Arewa, ko fastar hoton Buhari dan adawa ya keta, so sai an samu wani dan Buhariyya ya yi shahadar-kuda ya keta masa riga.
Amma yanzu ko ashana ka kyarta ka banka wa hoton sa wuta a tsakiyar kasuwa, ba wanda zai banka maka zagi.
Irin yadda dandazon jama’a suka taru a kan titin Court Road a Kano, su na rera wakokin zagi da cin mutunci ga Buhari, a lokacin da aka gurfanar da Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekaru a kotu, hakan ya tabbatar da raguwar farin jinin Buhari a Kano da kuma Arewa.
Sannan kuma an rika bin cikin birnin Kano a jikin bangaye da katangu ana rubuce-rubucen janyewa daga goyon bayan Buhari.
Duk ma dai yadda za a kalli nasarori da matsalolin Gwamnatin Buhari a cikin shekaru uku. Alamomi bayyanannu sun nuna raguwa farin jinin APC aka fi gani a sarari, ba karuwar farin jinin jam’iyyar ba.
Sai dai me, zaben 2019 shi ne zai yi alkalanci.
Discussion about this post