Yadda ta kaya dalla-dalla tsakanin JOHESU da gwamnatin tarayya, kwanaki 40 da fara yajin aiki

0

Yajin aikin da ma’aikatan asibitocin kasar nan karkashin kungiyar JOHESU suka shiga tun a ranar 17 ga watan Afrilu ya zama abin tashin hankali, fargaba da saka mutane cikin dimuwa da damuwa a kasar nan musamman yadda yanzu haka yajin aikin ya kai kwanaki 40 kenan ana yi.

Abin da ke dada tada wa mutanen Najeriya hankali shine a kullum sai kaji maimakon ace an warware kullin ne, sai kara cikwuikuyewa al’amuran su ke yi ba a gaba ba a baya.

Abu dai kamar wasa, maganar ta na neman ta gagari gwamnatin Najeriya. Ministan Kiwon Lafiya ya kasa kulla wani abin azo agani, abin sai kara faskara ya ke yi.

Idan ba a gaggauta duba wannan matsala ba, toh fa allura zai hako garma, domin kuwa kusan dukkan asibitocin da ke kasar nan sun bi sahun ‘yan kungiyar. Idan ka tafi asibitocin kasar nan za ka ga a kulle suke.

Mutane na kokawa kan rashin maida hankali da gwamnati batayi ba na ganin an kawo karshen wannan yajin aiki.

Duk da cewa ‘yan kungiyar sun yi ta nanatawa cewa su ba so a maida su mataki daya da likitoci suke kira a yi musu ba, su ko likitoci tuni sun harzuka sun wasa takobinsu sun gwaggwalo idanu, suna ta hura hanci cewa kada gwamnati ta kuskura ta amsa kukan ma’aikatan asibitocin kasar nan.

Likitoci har barazana suka yi na idan har gwamnati ta yi amsa su, za su fara yajin aiki.

A takaice ga yadda akayi ta kai ruwa rana tsakanin bangarorin da ba sa ga maciji wato kungiyar ma’aikatan kiwon lafiya JOHESU da bangaren gwamnati cikin kwanaki 40 da suka fara yajin aikin.

17 ga watan Afrilu:A wannan rana ne kungiyar JOHESU wato kungiyar ma’aikatan asibitocin gwamnati suka fara yajin aiki na gama gari. Sannan a wannan rana ne kungiyar likitoci (NMA) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi watsi da bukatun kungiyar.

Ranar 18: Gwamnati ta yi wa ma’aikatan kungiyar barazaran hana su albashin su idan har basu janye wannan yajin aiki ba.

Ranar 21: Kungiyar JOHESU ta ki janye yajin aikin sannan ta kira barazanar da gwamnati ta yi mata cewa tabarmar kunya ce.

Ranar 23: Gwamnati ta amince ta kafa kwamiti domin duba kuka da bukatun kungiyar JOHESU.

Ranar 26: PREMIUM TIMES ta ruwaito wasu matsaloli biyar da ka iya faruwa a fannin kiwon lafiyar kasar nan idan ba a kawo karshen yajin aikin JOHESU ba.

Ranar 29: Gwamnati ta tattauna da wakilan kungiyar JOHESU.

Ranar 1 ga watan Mayu: Kungiyar JOHESU ta karyata butun da gwamnati ke yi cewa ta biyan bukatun kungiyar har 14 cikin 15 da suke kira a yi musu.

Ranar 5: Gwamnati da JOHESU ba su daidai ta ba bayan zama da suka yi.

Ranar 9: Ma’aiktan asibitocin jihohi da kananan hukumomi sun bi sahun yajin aikin.

Ranar 10: Kungiyar likitoci ta yi wa gwamnati barazanar shiga yajin aiki idan gwamnati ta biya bukatun kungiyar JOHESU.

Ranar 13: Gwamnati tayi wa JOHESU tayi.

Ranar 14: Likitoci sun zargi JOHESU da muzguna musu da marasa lafiya a asibitocin kasar nan.

Ranar 15: Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya yi kira ga shugabannin asibitocin mallakin gwamnati a kasar nan da su samar wa likitoci da tsaro a wuraren aiyukkan su don gujewa barazanar ma’aiaktan JOHESU

Ranar 17: JOHESU ta zargi gwamnati da ministan kiwon lafiya kan rashin maida hankali kan ganin an biya musu bukatun su.

Ranar 18: JOHESU ta yi kira da a tsige ministan lafiya Isaac Adewole saboda nuna son kai da kin tabuka komai kan wannan yajin aiki.

Ranar 24: Kungiyar likitoci ta soki kungiyar JOHESU na kira a tsige Adewole

Ranar 25: Shugaban majalisar datijai Bukola Saraki ya gana da Adewole, ministan kwadago Chris Ngige da wakilan kungiyar JOHESU domin samun mafita ga yajin aikin.

Ranar 26: JOHESU ta tabbatar da samun umurnin ta janye yajin aikin amma ta ce ba za ta bi umarnin kotu ba.

Share.

game da Author