Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa Othman Abubakar, ya bayyana cewa akalla mutane 24 ne suka rasu a harin da wani dan kunar bakin wake ya kai wani masallaci da ke kasuwar ‘Yan gwanjo dake garin Mubi a daidai suna sallar Azahar, Sannan kuma wasu sama da 50 sun sami rauni.
Mazaunan wannan kasuwa sun shaida wa wakilin mu cewa wani matashi ne da bai wuce shekaru 17 zuwa 19 ba ya bi sahun masallata ashe daure a kugun sa jigidar bama-bamai ne.
” sai da akayi raka’a biyu tukuna sai ya tada bam din.” Inji Wani Dan kasuwa.
Yanzu dai gwamnatin jihar ta aika da jami’an bada agajin gaggawa domin taimakawa wadanda suka sami rauni sannan gwamman jihar ya mika sakon jajen sa ga ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukan su.