Jam’iyyar APC a jihar Kaduna ta gargadi sanatan dake wakiltar Kaduna ta Arewa a majalisar Dattawa da ya shiga taitayin sa ko ya kuka da kan sa.
Sakataren Jam’iyyar Yahaya Baba Pate ya bayyana haka da ya ke hira da manema Labarai a ofishin jam’iyyar dake Kaduna.
Baba Pate ya ce jam’iyyar APC a jihar Kaduna ta dade da dakatar da sanata Hunkuyi, bashi da damar hada wani gangami da sunar shi dan jam’iyyar APC ne.
“Eh shi dan jam’iyyar APC ne, amma kuma an dakatar dashi tun a watan Fabrairu. Saboda haka bashi da hurumin yi wa jam’iyya katsalandan a shirye-shiryen zaben wakilai da zata yi a jihar.”
Idan ba a manta ba, a karshen makonnan ne wasu gungun yan taratsi suka tarwatsa gungun ‘yan jam’iyyar APC tare da sanata Suleiman Hunkuyi a Kaduna.
‘yan taratsin dai sun shigo wurin taron ne suna cewa “Kaduna sai Uba Sani, Kaduna sai El-Rufai” kamar yadda kamfamin dillancin labarai ya ruwaito.
Daga karshe Pate ya ce jam’iyyar ba za ta zura ido ta bari wasu na kokarin tada zaune tsaye a jihar ba da sunan ‘yan jam’iyyar su ne, cewa lallai za su dau mataki kan haka.