An bindige mashawarcin Gwamnan Bayelsa

0

‘Yan sandan Jihar Bayelsa sun bazama neman wanda ya bindige mashawarchin gwamnan jihar, Seriake Dickson jiya Talata da dare.

Wanda aka bindige din mai suna Ebikimi Okoring, an rantsar da shi ne cikin watan da ya gabata, ko kama aiki bai kai ga yi ba.

An harbi shi da misalin karfe 1:00 na dare a garin su da ke cikin Karamar Hukumar Kolokuma/Opokuma kimanin kilomita 20 da Yenagoa, babban birnin jihar.

Kwamishinan ‘Yan sandan Bayelsa, Don Awunah, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ya bada umarnin sai an kamo duk wadanda ke da hannu wajen kisan mamacin.

“Mun gano cewa ya samu dan sabani da wasu mutane dan lokaci kadan kafin a bindige shi. Don haka mun baza komar mu kuma ba za mu zauna ba har sai mun kamo wadanda ke da hannu wajen kisan shi.”

Share.

game da Author